• Sun. Nov 10th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Maganar Soyayya Tsakanin Rarara Da Aisha Humaira Gaskiya Ta Fara Yin Halinta

ByLucky Murakami

Nov 13, 2022

Mawaki Dauda Rarara Kahutu, Ya Bayyana Alaqar Dake Tsakaninsa Da Jaruma Aisha Humaira, Mawakin Ya Bayyana Hakan Ne A Hirar Da Sukayi Da Jaruma Hadiza Gabon, Inda A Shirin Nata Take Zantawa Da Jarumai Da Kuma Mawaka.

Aisha Humaira Dai Tana Daya Daga Cikin Jarumai Mata Da Tauraruwarsu Ke Haskawa A Masana’antar KannyWood, Sai Dai Anga Lokaci Guda Ta Jingine Harkar Fina Finan Ta Koma Karkashin Kamfanin Mawakin Wato Rarara Kahutu.

Kafin Komawarta Karkashin Kamfanin Na Mawakin, A Baya Ana Yawan Ganinta Da Mai Shirya Fina Finan Nan. Abubakar Bashir Mai Shadda, Inda Bayan Auren Na Mai Shadda Ne Kwatsam Sai Akaga Ta Koma Bayan Mawaki Rarara Kahutu.

Hakan Yasa Mutane Su Fara Zargin Cewa Kamar Akwai Soyayya Mai Karfi A Tsakaninsu. Ta Yanda Ko Da Yaushe Ake Ganinsu A Tare.

Shin Akwai Soyayya Ne TsakaninKa Da Jaruma Aisha Humaira?

Wannan Itace Tambayar Damai Gabatarwa Ta Mishi A Cikin Shirin. Inda Mawakin Ya Bada Amsa. Ga Abin Da Mawakin Ke Cewa A Wanann Bidiyon.

Mawakin yace yayin da akayi masa tambaya cewa shin dagaske ne suna soyayya da wannan jarumar wanda ya bayyana cewa daman ai babu yadda za’a yi ace kuma tare da mutum mai amana da wannan jarumar yace baya sonta.

Cikin ikon Allah kuma sai gashi sun bayyana cikin wannan shigar wanda hakan ya bawa mutane mamaki kuma yasa suna zargin lalle daman akwai wata kullalliya a kasa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *