• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Maganar Tsayawa Takara A Zaben 2023 Yan Kannywood Sun Sake Zage Damtse

ByLucky Murakami

Sep 13, 2022

Da alama kungiyar 13×13 a karkashin jagorancin fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara da ta YBN, wato Yahaya Bello Network sun sake sa zare.

’Yan Masana’antar Kannywood sun dade suna bayyana cewa, suna shiga harkokin siyasa ne domin su kawo ci gaba ga masana’antar.

Da alama kungiyar 13×13 a karkashin jagorancin fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara da ta YBN, wato Yahaya Bello Network sun sake sa zare.

’Yan Masana’antar Kannywood sun dade suna bayyana cewa, suna shiga harkokin siyasa ne domin su kawo ci gaba ga masana’antar.

Sai dai Aminiya ta lura duk da cewa ana kawo ci gaban, ana samun baraka mai yawa a tsakanin jaruman masana’antar.

Aminiya ta ruwaito yadda aka samu baraka, har ta kai ana yi wa juna gugar-zana a tsakanin ’yan masana’antar, musamman tsakanin ’ya’yan kungiyar 13×13 da ’ya’yan kungiyar YBN.

Ana samun gugar-zanar ce wajen raba kyaututtuka kamar motoci da babura da gidaje da kudade, wanda yawanci kowane bangare yake yi ga mabiyansa.

Aminiya ta kuma ruwaito yadda da yawan ’ya’yan masana’antar ba sa son tsayawa takara, inda suke fi son tallata wasu ’yan takarar, su samu kudade su kawo masana’antar, su ba ’yan bangarensu.

Bayan kammala zabubbukan fid-da-gwani, an yi zaton barakar ta kare, inda aka yi tunanin za a dawo a hade a tsakanin kungiyar 13×13 da ta YBN, ganin cewa dukkansu APC suke tallatawa, amma sai ga wata barakar ta kara kunno kai a kan dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar APC.

Alamar baraka

A ranar Talatar da ta gabata ce Khalid Yusuf Atta, wanda aka fi sani da Khaleedo da ke cikin furodusoshin shirin Alaka mai dogon zango ya wallafa bidiyonsa da jagoran kungiyar YBN, Abdul Amarta Maikwashewa da rigar YBN a shafinsa na Instagram sannan ya rubuta cewa, “Ba mu fara don mu daina ba. Nan ne layinmu,”

Ya kara da cewa, “Alheri cikin cokali ya fi sharri cikin duniya ko a wajen Ubangiji. Ba mu fara bin tafiyarka don wata rana mu gaza ba ko kuma wani rudin abin duniya na wani lokaci ya rude mu ba, ka ba mu muhimmancin da ko a mafarki ba mu yi tunanin samun sa ba! Ba ka taba burus da bukatunmu ba, halaccin da ka mana ba zai ba mu damar a je wani gurbi don cutar da kai ba. kara hakuri Kwashewa har gobe kai kake bin su bashi kuma da bazarka suke rawa.”

Sai dai wani mai suna Ahmed New boy ya mayar masa da martani cewa, “To uban ’yan habaice-habaice.”

Wannan rubutun na Khaleed ya zo ne kwanakin kadan bayan kungiyar 13×13 ta yi taron raba motoci da sauran kyaututtuka ga wadanda suka lashe Gasar Rawa ta Jagaba Shi Ne Gaba.

Asali ita dai kungiyar YBN tana tallata Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ne a matsayin dan takarar Shugaban kasa, wanda ya sha kaye a zaben fid-da-gwani.

Sai dai a lokacin da ita kungiyar 13×13 ta su Rarara ta dauki tallar dan takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar ADP, Malam Sha’aban Sharada, ita kuma ta YBN, kwatsam sai aka gan su da dan takarar APC, kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Yusuf Gawuna.

Daga cikin wadanda Aminiya ta hango tare da Gawuna akwai jagoran YBN, Abdul Amart da Ali Nuhu da Mommee Gombe da Maryam Yahaya da sauransu Shi dai Dauda Rarara a wani faifan bidiyo da Aminiya ta gani ya ce, sun dauki tafiyar Sha’aban Sharade ce domin ya ba su muhimmanci.

A cewarsa, “Dole mu hada kanmu domin ciyar da masana’antar gaba. Na ce duk wanda yake son sulhu da ni, to ya dauki wasu daga cikin ’yan siyasar (takara) nan.”

Haka kuwa aka yi, domin bayan amincewa za su yi tafiyar Sha’aban, sai ga fastocin takara na Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi sani da Abale ko Daddy Hikima yana takarar Majalisar Wakilai a Mazabar Kumbotso da Aminu Ala domin wakiltar Nasarawa a Majalisar Wakilai da kuma Naziru dan Hajiya domin wakiltar Kura/ Madobi/ Garun Malam a Majalisar Wakilan.

Wannan ne karo na farko da aka samu ’yan Kannywood da dama da za su shiga a dama da su a zabe ba kamar a baya ba da suka fi zama ’yan talla.

Dalilin da na fito takara Dan Hajiya

Da yake tattaunawa da Aminiya, Forodusa Naziru dan Hajiya, wanda ya yi takarar Majalisar Jihar Kano a Jam’iyyar APC ya ce, yana da yakini dari bisa dari cewa zai yi nasara, sannan sauran ’yan uwansa ma za su yi nasara.

“Na yi mamaki, duk da cewa lamarin Allah ba abin mamaki ba ne, na yadda mutane suka karbi tafiyar nan.”

Game da batun ’yan fim ne suke takara a Jam’iyyar APD, sai ya ce, “Ai dokar kasa ta ba kowa dama ya yi takara.

Sannan dama can muna da mutane da suke kaunar mu. Muna shiga kauyuka da lungu da sako domin shirya fim.

Ko kwanakin baya akwai wani kauye da muka je, dan fim ne ya gina musu masallaci. Don haka, muna da mutane sosai.

Sannan dama ya kamata a rika samun wakilci daga kowane bangare. Ya kamata ’yan jarida da sauransu kowa ya rika samun wakilci a cikin siyasar nan.”

Da yake sanar da takararsa, Aminu Ala ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa, “Mulki na Allah ne, Yana bai wa wanda Ya so a lokacin da Ya so.

Mun fito da karfin Allah tare da goyon bayan mutane don mu wakilci mutane daga cikin mutane zuwa ga mutane don mutane. Kamar yarda Allah Ya ba mu damar bayyana kai a rukunin masu shirin wakilcin jama’a.

Muna neman tallafawar Allah a cikin dukkan motsi da gilmawarmu a kan wannan kudiri.

Allah Ka kaddara wannan yunkuri ya zama alheri ga al’muma Allah Ka sa ya zama ci-gaban kasata, Allah Ka sa ya zama alfanu a gare ni da al’ummar yankin Nassarawa kafataninsu.”

Shinkafa da wake kungiyar 13×13 za ta yi

Sai dai Aminiya ta lura kungiyar 13×13 ta shirya yin siyasar shinkafa da wake ne a zabubbukan shekarar 2023.

Abubakar Bashir Maishadda ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Ok, na gane.

A Kano za mu yi ADP, (Malam Sha’a’aban Sharada).A Najeriya kuma za mu yi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a APC. Hakan ya yi min.”

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *