• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Mai Sana’ar Rake Yana Samun Naira Dubu Daya A Rana Yafi Mai Digiri Dan Zaman Banza

ByLucky Murakami

Aug 5, 2022

Idan Mukayi Duba Da Yanayin Da Rayuwar Matasan Nigeria Take A Yanzu Musamman Wadanda Sukayi Karatun Zamani, Yadda Suke Fama Da Rashin Aikinyi Daga Gwamnatin Kasar. Shafin dalatopnews.com ne ya rawaito wannan labari.

Matashi Abdurrahman Birnin Kudu Yayi Tsokaci Akan Rayuwar Matasanmu A Yanzu Musamman Wadanda Suka Kammala Karatun Jami’a.

Yadda Bayaninsa Ya Fara Dacewa:

IDAN KUNNE YAJI JIKI YA TSIRA

Daga karfe 9:00am na safiya zuwa karfe 1:00pm na rana, awa hudu kacal matashi burkila mai sa tiles, yasaka 30 meters at N350 each making N10,500.

Idan kullum zai samu aikin N5000 ma, a wata yana da N150,000. Amma da Degree dinka kana aiki Local government ko Jiha ana biyanka N65,000 ko N80,000 kana karya hula da k’aro wai Kai ma aikacin gommnati.

Maginin da ke gini a kirge, each Blocks N40. Shi da leburansa sun gina 300 an biyasu N12,000.

Kaddara aikin N4000 suke a rana, zasu samu N120,000 kana kwance jiran tsammani da kwalin Diploma wai ai kai dan boko ne kafi karfin daukar Cement.

Mai rake yana kasawa ya samu N1000 a rana ya koma gida. Kai da kwalin degree kana bin inuwar bishiya kana zama ba ko sisi.

Mutum yana da jarin N40,000 yana sarar kaji ya bi kasuwa ya ci ribar N3000 ko N2000 ya dawo gida.

Kai dan boko ka kasa aure wai ba ka da sana’a, kana bin dan siyasa tare da lissafin idan ya ci ya baka aiki ko a shiryo scopes a ba ku kudi.

Ko Kuma Yan Siyasar da Basu San darajar Mutane ba, kullum Yaudara Matasa suke, Matasa Sun kasa amfana kansu sai bata Lokaci.

Da yawa talauchi a gindin yan boko yake karewa, musamman a arewa, bisa dogaro da kwalin degree ko NCE.

Zamani ya canza, wajibi ne garemu matasa muma mu canza tunani.

Kwalin degree da bautar yan siyasa ya bar zukatanmu, a koma neman na kai.

Akarshe ina Kira ga masu ruwa da tsaki Dama masu hannu da shuni da su rika wallah fa wata gidauniya domin amfani Matasa da ma marassa karfi domin suna samun jari da kuma wayewar kai dangane da Zamani tafiskar dogaro dakai.”

Meye Ne Ra’ayinku?

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *