Wani yanki daga cikin shirin fim din Gurnani da wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta ta TikTok, Nura Nabala ya wallafa ya yi matukar daukar hankulan jama’a, Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.
A bidiyon anga inda jarumi Salisu S Fulani ya bukaci Mama Daso a matsayin ‘yar aikin gidansu da ta siyo masa fim da mujallar batsa tare da sanar da ita yadda zata yi sumogal dinsu ya amsa.
Jaruma Saratu Gidado, wacce ta kasance a cikin shirin ta yi martani ga wata ma’abociyar TikTok mai suna Leematu, wacce tayi tsokaci karkashin bidiyon inda tace:
“Wannan su ne masu koya tarbiyya?
“Eh sun koya mana kuwa Alhamdulillah amma kallar fim naku ma yana taka rawa.”
Daga nan Saratu Gidado ta mayar mata da martani inda tace:
“Wa ya matsa muku dole ku kalla?”
Leematu ta bata amsa da cewa:
“Kiyi hakuri, ni bana kallon fina-finan Hausa wallahi. Ni bazan iya cacar baki da ke ba saboda kin isa haifar kama ta. Kiyi hakuri.”
Take Daso ta kara bata amsa da cewa:
“Ba tarbiyya muke koyarwa ba, iyayenku ya kamata su koya muku tarbiyya, mu sana’a muke yi.”
Anan ne wani Young Alaji ya ba Daso da martani inda yace:
“Allah wadaran naka ya lalace, indai wannan ne irin taku sana’ar, Allah wadarai dai. Domin lallai wannan yana daga cikin yada alfasha.”
Wannan ba shi ne karon farkon da ‘yan fim da su ke bayyana cewa sana’a su ke yi ba koyar da tarbiyya ba, akwai wata hira aka yi da Shehu Hassan Kano, inda yace nishadantarwa suke yi.
Ga Bidiyon Anan Zaku Iya kalla: