Wani matashi ya yi karar iyayen budurwarsa a gaban Babbar Kotun Shar’iar Musulunci da ke Hotoro a Kano yana neman kotun ta hana su aura.
Wani matashi ya yi karar iyayen budurwarsa a gaban Babbar Kotun Shar’iar Musulunci da ke Hotoro a Kano yana neman kotun ta hana su aurar da ita ga wani saurayin daban..
Tunda farko matashin mai suna Imam Mukhtar Dala ya yi karar budurwarsa Muhassin Auwal Dala da mahaifinta A.A. Dala da kakanta Sani Mai Alawayyo da kuma aminin babanta, Alhaji Audu, inda ya nemi kotu ta dakatar da auren da ake kokarin yi wa Muhasin din saboda shi ne ya yi hidimar da zai aure ta.
Haka kuma ya nemi a hana Muhasin Dala zuwa wurin kowane mutum don daura mata aure.
A zaman kotun lauyoyin wadanda ake kara karkashin jagorancin Barista Muhammad Lagazan Abubakar suka nemi kotun ta cire sunan wasu daga cikin shari’ar da suka hada da kakan yarinyar Alhaji Sani Mai Alawayyo da kuma aminin mahaifinta Alhaji Audu kasancewar ba su da hannu a cikin shari’ar.
Barista Lagazan ya nemi kotun ta ba shi dama ya yi martani da baki sai dai kotun ta ki amincewa da bukatarsa, inda ta dage cewa a rubuce ake bukatar martanin nasa.
Shi ma lauyan wanda ya yi karar, Barista Mujiburrahman Ahmad ya nemi kotun ta ba shi lokacin yin nazari don mayar da martani game da bukatar lauyoyin wadanda ake kara na janye wasu daga cikin shari’ar.
Alkalin Kotun Mai shari’a Isa Salisu Kura ya dage sauraron karar zuwa ranar 30 ga Nuwamban nan.