• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Matashi Yasha Zagi Bayan Kure Rahama Sadau Akan Sarkar Kafarta

ByLucky Murakami

Jul 16, 2022

Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumunta ta Twitter ya wallafa hoton jaruma Rahama Sadau sanye da sarkar kafa inda ya bukaci karin bayani kan dalilin da yasa take sanyawa.

Babu bata lokaci kuwa aka dinga bashi amsa game da fahimtar jama’a kan matan dake saka sarka kafar. Wasu sun ce ‘yan madigo ke sanyawa yayin da wasu suka ce kwalliya ce kawai ta mata wacce addini bai haramta ba.

Wani kuwa da yace yayi bincikensa a google, yace ma’ana biyu gareta. Idan mace ta sanyata a kafar dama toh tana bayyana ita budurwa ce kuma tana neman miji, idan kuwa a hagu ne, toh mata aure ce. Sai yace a dama Rahama Sadau ta saka tata, ga me sha’awa sai ya taya.

Ganin wannan, jaruma Rahama Sadau ma ta tanka inda ta bada amsa da cewa: “Ya kai anonymous, wannan sarkar gwal ce mai matukar tsada, da fatan na amsa maka tambayarka.”

Sai da babu jimawa wani daga cikin masu tsokacin ya mayar mata da amsa cewa, “Don uwarki aka ce ki saka a kafa?”
Babu bata lokaci jarumar taje ta mayar masa da martani kamar haka: “Eh Fa, Uban babanka ne yace in saka a kafa.”

Babu jimawa aka fara cece-kuce kan lamarin, inda da yawa daga cikin jama’a ke goyon bayan jarumar da ta rama zagin uwarta da aka yi.

Wasu kuwa cewa suka yi duk da bai kyauta ba, bai dace ta biye masa har tayi masa martanin zagi ba. Hakan yana nufin sun zama daya kenan.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *