• Fri. Jun 21st, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Mene Ne So, Soyayya, Shakuwa?

Soyayya da shakuwa

Assalamu Alaikum, Barkanmu da kasancewa a wannan shafi mai suna SOYAYYA DA SHAKUWA, wanda zai mayar da hankali kacokaf kan Soyayya da kuma abubuwan da ta kunsa musamman a wannan zamani da muke ciki. Da yardar Allah wannan shafi zai rika zauwa maku kowane mako.

Shiri ne dai zai rika duba kan abubuwan da suka shafi Soyayya, musamman yanda Soyayya take gudana a wannan zamanin.

Zamu rika tattaunawa tare da ku ta hanyar yi muku tambaya, don ku ba mu amsa, ama zai kasance kan soyayya ne kawai.

Har ila yau, shafi zai kusnhi kirkirarrun labarai wadanda suka shafi soyayya duk don karuwa da juna da kuma nishadanta da ku. Baya ga haka, za mu yi nazarin kan labarin da muka bayar domin yin fashin baki a kai.

Tun da mun kira da shafin da Soyayya Da Shakuwa, zan dan yi waiwaye domin bayyana ma’anar SO, SOYAYYA da kuma SHAKUWA. Wanda duka wadannan guda ukun suna da tasu ma’anar ta musamman.

Menene So?

Shi dai so ya kasu kashi-kashi a takaice, shi ne zuciya ta ji tana son wani abu, hakan na iya faruwa ta hanyar jin jin labarin mutum, sauraron muryarsa ko kuma ganinsa a zahiri. A irin wannan yanayi dan’adam yake tsintar kansa da shaukin son kasancewa tare da abin da ya kamu da sonsa.

Allah (SWT) shi ke da ikon sanyawa dan’adam soyayya wani a zuicya, shi ya sa wasu lokuta da dama, idan aka kamu da so ba a iya rabuwa, domin ba yin mutum ba ne, yin Allah ne.

Soyayya

Shi ma ya kasu kashi-kashi sai dai in yi bayani a takaice tun da na gaban zamu rika tattaunawa a kai.

A wata ma’anar, Soyayya na nufin isar, watau yin sa a aikace musamman idan wanda ake so ya amince. Da zarar haka ta faru, shi ke an wannan So din ya koma soyayya. Ba a yin soyayya dole sai zukata biyu sun aminta juna, idan ta kasance bangare daya ne kawai yake fama da so, dan’uwansa bai damu ba, to wannan ba soyayya ba ce.

Soyayya ba ta cika dole sai bangarori biyu sun damu da juna, ta hanyar kyautatawa, kulawa da kuma begen ganin juna ko jin muryoyin juna.

Shakuwa

Shakuwa na da dangantaka ko na ce alaka da soyayya, domin duk wanda ya ce soyayya dole a samu SHAKUWA a cikinta. Ba lallai ne duk wanda ya shaku da wani to dole sai sun yi soyayya ba. Sai dai wata shakuwar takan koma soyayya dalilin kulawa da juna tsakanin saurayi da budurwa.

Amma soyayya sam ba ta yiwuwa matuka babu shakuwa, domin ita tamkar wani sinadari ne yake kai zuciyoyi dausayin da za su fara tunanin ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba.

A takaice, Shakuwa tana nufin kasancewa tare da abinda ake so na tsawon lokaci ba tare da an gundiri juna ba.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *