Abubuwan ban mamaki da al’ajabi basa karewa yayin da wani magidanci mai suna Yusuf Mohammed ya riki Kotun Magajin Gari dake Kaduna da ta tilasta wa matarsa Murjanatu Nasiru ta biya shi naira miliyan 1.6 diyyar auren sa da ta ce ba ta yi kuma.
Majiyar amihad.com ta tabbatar mana Yusuf ya shaida wa kotu cewa ba shi ne ba ya son auren ba, Murjanatu ce ba ta so, saboda haka dole ra biya shi sadakin da ya biya na auren ta sannan kuma da wasu kuɗade da ya easa a dalilin aurenta da yayi.
” Bayan sadakin naira 50,000 da na biya, akwai yayana da yake bani naira 35,000 duk wata amma a dalilin auren Murjanatu da nayi ya daina bani tun daga 2018. Saboda haka dole ta biya ni wannan kudaɗe tukunna. jKamar yadda majiyarmu jaridar Premium Times ta rawaito.
Lauyan da yake kare Murjanatu ya ce babu wannan alkawari a tsakanin Murjanatu da Yusuf.
” Murjanatu ta ce ba ta kaunar zaman aure da Yusuf saboda haka take neman kotu ta raba su, domin bata so ta yi abinda ba haka ba ta rika saba wa Allah.
Alkalin kotun Rilwanu Kyaudai ya dage Karar zuwa 15 ga watan Satumba domin cigaba da shari’ar.
A bisa shari’ar Musulunci mace na da damar cewa bata yin aure da wani idan zaman nasu bai gamsar da ita ba, amma kuma sai anbi hanya ta koyarwar Musulunci.