Matar Aure ta roki da Kotu ta raba Auren su da Mijinta Saboda Ba ya Cefane.
Matan mai suna florence ideyi, ta roki kotu taraba auren su da mijinta Victor saboda baya fita nema kuma yana yawan zuke-zuken hayaki.
Matan wanda ‘yar kasuwa ne ta fadawa kotu ta raba auren nasu da mijinta a ranan Litinin a kotun Igando dake jahan lagos, matan tana mai cewa maigidan nata yaki aiki tsawon shekara 10.
Misis Ideye, ta kumayi zargin cewa mijin nata nason shaye-shaye da yawan fadace-fadace. tace mijin nata ya dogara ne akan kanin Shi wanda ya kasance dan kwallon kafa don kula da iyalin Shi.
Victor yace yana daukan dawainiyan iyalan shi don kanin Shi na aike mishi kudi sosai, yace har shaguna guda 5 yabudewa matan nashi da sana’o’i iri-iri.
Mijin yace abinda ya fahimta da matar tashi shine soyayyan kudi take domin yanzu kanin nashi Ya daina aike mishi kudi.