• Thu. May 23rd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Muna Bukatar Mazajen Aure Inji Jaruma Rsshida Mai Sa’a

ByLucky Murakami

Aug 18, 2022

Labarin da amihad.com take samu shine tsohuwar jaruma a Masana’antar fina-finai ta kannywwod, Rashida Adamu Abdullahi, wadda aka fi Sani da Rashida Mai Sa’a, ta yi yekuwar neman mijin aure ga duk wanda ya shirya auren su ya zo sun shirya.

Jaridar Dimukaradiyya ta rawaito cewa jarumar ta Kara jaddada maganar ta ne bayan wadda ta yi a shafukan ta a lokacin tattaunawar su da wakilin jaridar , in da ta ke cewa:

“Jama’a su Sani ni Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a da kawaye na su Hadiza Kabara da Teemah Yola da Jamila Nagudu, duk cikakkun Zaurawa ne idan akwai Mai son wata a cikin mu to ya fito mun shirya, Kuma zan tsaya Wa mashi, a matsayina ta shugabar su, don haka idan har da mai bukatar auren mu, to ya fito mun shirya”.

Ganin cewar a na yi wa maganar ta kallon kamar da wasa take yi don haka ba Lallai ba ne a samu wanda zai Taya din, Sai ta ce:

“Babu maganar wasa in dai mutum ya shirya to ya same ni duk wadda ya ke so a cikin mu idan an daidaita abin ba zai zo da wahala ba, don haka maza kada su dauka da wasa mu ke yi, mun shirya auren ga duk wanda ya shirya zai auren mu, in dai da gaske ya ke yi. “

 

Duk Da Nayi Aure Zan Cigaba Da Fitowa A Fim Din Kwana 90 Inji Rahma Mk

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, an yi shagalin bikin ne a gidan su da ke birnin Kano a sirrance don ba a bayyana wa mutane da dama ba.

Rahma Mk wadda ita ke fitowa a matsayin matar Bawa mai kada tsohon gwamnan jihar Alfawa a cikin shirin na kwana chasa’in.

Rahotanni sun nuna yadda aka yi shagalin bikin a gidan su da ke cikin garin Kano cike da sirri don ba kowa ya sani ba.

Tuntuni an samu labari a kan batun auren jarumar amma ba ta fadi lokaci da kuma wanda za ta aura ba, hakan ya sa mutane su ka dinga mamaki.

Yayin da manema labarai sun bukaci jin ta bakin jarumar,inda ɗ ta bayyana cewa:

“Dama na shaida cewa zan yi aure tun kwana 3 da su ka gabata, kuma ga shi Allah ya tabbatar kuma ya cika min buri na.”

Ta kara da addu’ar Allah ya ba ta haihuwa kuma ta yi fatan mutuwa a dakin mijin ta.

Batun fina-finai kuma ta ce za ta ci gaba da fitowa a shirin Kwana Casa’in, amma sauran babu tabbas.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *