Entertainment

Musha Dariya Labaran Ban Dariya Da Barkwanci

A wannan shashe na musha dariya amihad.com ta zage damtse wajen kawo muku labaran barkwanci masu matukar burgewa da nishadantarwa.

Saboda haka ku gyara zama domin samun nishadi ta hanyar karanta labaran da zamu gabatar muku a cikin wannan rubutu da amihad.com ta dauki nauyi.

Labari Na Daya

Taken Wannan Labarin Jana’izar Kare

A wani gari ne akayi wani mutum mai kudi sosai sunansa mallam Sadi. Yanada kudi baida iyali sai wani katon bakin karen sa.

Saboda son dayake nunawa Karen har anfara zarginsa akan watakila Karen na tsafi ne. Wannan online gidan caca Book of Dead yana ba da ramin lantarki sama da 500 kuma yana buɗewa 24/7.

Rana daya sai aka wayi gari Karen ya mutu, toh abunka da mai kudi sai yatara yan unguwarsu yace ayiwa karensa jana’iza kamar yanda akewa mutane. Aka taru anawa Karen jana’iza sai labari yaje kunnen sarkin garin.

Sarki ya taso cikin baccin rai yazo kofar gidan attajirin nan da dogaransa.

Yana zuwa ya fara fada kamar haka:

Sarki: “kai awane gari kataba ganin anyiwa kare jana’iza?” Yafada cikin fushi.

Attajiri: “Ranka yadade dama Karen nan ne kafin ya mutu yace inya mutu akayi jana’izarsa to abaiwa sarki miliyan biyar jama’a kuma abaiwa kowa miliyanbiyu biyu.

Sarki: cikin rawar jiki ya amsa “Wato shi marigayi din ne yafadi hakan?”

Attajiri “Eh”

Sarki: “Toh Allah Ya jikan Malam kare, maza mu kaishi makwancinsa.

Hahahahaha. Duk wanda yakaranta shima anbashi miliyan biyu!

 

Labari Na Biyu

Taken Wannan Labarin GAYE A RESTAURANT

Wani gaye ne ya shiga Restaurant ya zauna kusa da wasu yan mata, Ga sauti yana tashi da Karfi DOOM DOOOM, duk lokacin da sauti zai ce DOOM kawai sai ya saki Tusa Dumm!

Sai ya basar,sai ya kalli yanmatan sai yaga yan matan suna Satar kallonsa, sai ya sake sakin wata DAMM, ya sake sakin ta 3 DARAM sai kawai yaga kowa na kallonsa.

Sai ya tuna ashe AIRPHONE yasaka a kunnen sa yake jin sauti shi kadai. Wai idan kaine ya zakayi?

 

Labari Na Uku

LABARIN WANI BAZAZZAGE

Wani shakiyin Bazazzagi ne ya yi dinkinsa babbar riga mai asake akan wata dalleliyar shadda ruwan kwai. Da ka ganshi ka ga mai hannu da shuni.

Ai kuwa sai ya nufi gidan abinci (Restaurant), ya samu waje ya zauna ya kwalawa mai restaurant kira da karfi ya ce “Hado min plate na Naira 2,000 kuma ki hadawa kowa da ke wajen nan plate na Naira 3, 000 saboda idan ina cin abinci, ina so naga kowa yana ci”.

Duk mutanen da ke wajen suka fara godiya yayin da mai restaurant ta zubawa kowa nasa ta kawo masa hadin girma. Shinkafa da dankalin turawa da farfesun kayan ciki ko kifi ko naman kai, ya dai danganta da abinda mutum ke so.

Kana ga hadin kwadon kayan lambu da a turance a ke kira da salad Bayan mutumin ya gama cin abinci sai ya kuma cewa mai abincin “kawo min abin sha na Naira 500 kuma ki baiwa kowa na Naira 1, 000 saboda idan ina shan abu, ina so naga kowa yana sha”.

Mai Restaurant ta kaiwa kowa kayan shaye-shaye kala-kala. Nan fa mutanen wajen suka barke da shewar “Allah ya kiyaye ka!” Bayan mutumin ya gama sai ya cewa mai Restaurant “kawo min resit na biya kudina kuma ki kaiwa kowa nasa resit ya biya kudinsa, saboda idan ina biyan kudina ina so naga kowa yana biyan nasa”.

Yanzu haka mutumin yana kwance a asibiti saboda dan karen dukan da masu gidan abinci da kuma mutanen da ya saka suka ci abincin da basu yi niyya ba suka yi masa Yanzu haka ni kuma ina kwance ina dariya, saboda idan ina dariya ina so na ga kowa na dariya.

 

Labari Na Hudu

LABARIN WANI BUZU DA BARAWO

Wani Buzu ne falke, ya rika bugun gaba yana cewa shi babu wanda ya isa ya yi masa sata. Ashe wani babban barawo ya ji haka, don haka sai ya sha alwashin sai ya yi masa sata.

Wata rana an ci kasuwa, Buzu ya sayar da kayansa duka, sai barawon nan ya sace masa kudi, ya bar shi da rakumi kadai, sannan kuma ya yi masa aski kwal-kwabo, a lokacin da yake barci.

Da safe, Buzu ya tashi ya ga cewa an yi masa sata sai ya yi ta mamaki, yana cewa: “Ni din ne za a yi wa sata? Can sai ya shafa kansa ya ji ba gashi, sai ya ce: “Haba, ashe ma ba ni ba ne!”

 

Labari Na Biyar

LABARIN WANI BABARBARE

Wani Babarbare ne aka kai shi asibitin mahaukata don a duba lafiyarsa ko ya warke. Da suka je sai ya kama wata bishiyar mangoro ya hau, tun da safe.

Aka yi, aka yi ya sauko ya ki sai da yamma sai ya fado kasa tik. Likitocin suka tambaye shi cewa: “Me ya sa ka fado kasa?” Sai ya ce: “Nuna na yi, shi ya sa na fado.”

Kamar yanda nace labaran guda biyar ne yau zamu kawo maku Qayatattun labarai ne guda biyar kuma cikin ikon Allah mun kawo kaman yanda munkace.

Dafatan kunjindadin wadannan labaran kuci gaba da ziyartarmu domin samun sabbin shirye shiryenmu masu inganci mungode sannan kutaimaka kumana share domin bamu qwarin guiwar kawo maku wasu labaran mungode.

Kuci gaba da kansacewa da shafin amihad.com domin samun labaran barkwanci na musha dariya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button