Musulmi Da Kirista Allah Duk Yana Ganin Mu A Matsayin Dai-Dai Ne – Sarkin Musulmi
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alh. Abubakar Sa’ad na III yace! Babu wanda zai iya kawar da Addinin Kirista Addinin Musulmi a kaf fadin Najeriya, bisani haka Allah ya haliccemu wuri guda.
Bugu da Kari Abubakar Sa’ad ya cigaba da cewa; Wani bai isa ya kawar da kowane addini a Najeriya ba, domin Allah ne ya yi mu, ya halicci wadannan addinai.
Ya kuma hada mu wuri daya, zaman lafiya nada matukar muhimmanci a gare mu mu cigaba da zama a matsayinmu na kasa daya Al’umma Daya, don haka kada mu bari wani ya yi amfani da addini ya raba kawukan mu.