• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Nasan Yadda Zan Gano Da Kuma Magance Matsalolin Nigeria – Bola Tinubu

ByLucky Murakami

Sep 5, 2022

Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin da zai kafa idan ya ci zaɓen 2023, za ta ƙunshi zaƙaƙuran mutanen da za su yi hangen nesan gano matsalolin da ƙasar nan ke fama da su, tare da magance su nan da nan.

Tinubu ya yi wannan bayani a Abuja ranar Asabar, lokacin da aka ƙaddamar da motoci masu ɗauke da tambarin kamfen na Gida-gida, wato “Door-to-Door Tinubu/Shettima 2023”, wanda ƙungiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihohin Arewa na APC su ka shirya.

Tinubu ya ce sannan kuma tawagar sa na da hazaƙar azurta Najeriya da ‘yan ƙasa baki ɗaya.

“Ai mu ne masu hangen nesan cikin jam’iyya. Mu na son ilmi mai inganci ga ‘ya’yan mu, mu na buƙatar ci gaban Najeriya da arzikin ƙasa musamman ta hanyar bunƙasa harkokin noma ta hanyar dabarun zamani.

“Mu na ji da kan mu cewa za mu iya. Mu na da abin da ake buƙata wajen masu irin wannan ƙoƙari da kishi. Mu na da wannan ƙudiri. Kuma mu na da wannan juriyar iya yin aikin.” Inji Tinubu.

Ya ƙara da cewa APC ba ta damu da PDP ba, ballantana ma ta tsaya ta na ce-ce-ku-ce da ita ba.

Ya ce a matsayin APC na jam’iyyar da ta ƙunshi masu tunani, ba ta buƙatar ɓata lokacin yin hayaniya da PDP, jam’iyyar da rigimar shugabanci ma kaɗai ya ishe ta.

“Kada mu riƙa surfa wa jam’iyyun adawa zagi. Ai mun fi su sanin ya-kamata. Mun fi su basira da nagarta. Ta mu ba irin ta su ba ce.

“Sun yi shekaru 16 su na mulki, amma a lokacin sun manta cewa akwai buƙatar jiragen ƙasa masu jigilar jama’a da kayan su a ƙasar nan.” Inji Tinubu.

Daga nan ya shawarci PDP cewa ta jira ta ga irin kayarwar da APC za ta yi mata a ranar zaɓen shugaban ƙasa.

Haka kuma Tinubu ya gode wa ƙungiyar ‘yan Majalisar Dokokin Arewa dangane da wannan yunƙurin haɗa kayan kamfen da su ka fara yi masa.

“Kun sauƙaƙa mana rayuwa, saboda ko sisi ba ku nema a wurin mu ba. Lallai ku ma ku na neman ganin Najeriya ta zama ƙasaitacciyar ƙasa.

Shi ma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya ce idan aka zaɓi Tinubu, za su gina sabuwar Najeriya.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *