Wata magana wanda Alhaji Atiku Abubakar yayi wanda ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta wanda yace duk zargin da akeyi a kansa ba gaskiya bane.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar lokacinda ya ziyarci wata kasa a kokarin takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.
Mista Abubakar shine yake neman takara a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) domin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Yayinda yake Magana a Ado Ekiti lokacin ganawar, Atiku yace zarge-zargen rashawa da ake yi masa karya ne ba gaskiya bane.
Ya kasance mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.
Atiku ya raba gari da ubangidansa jim kadan bayan zaben 2003 wadda PDP tayi nasara. Sai daga baya aka zarge shi da hannu a rashawa wadda majalisar dattawa ya bincike shi akai.
Majalisar dattawa a 2006 ta gudanar da bincike ta kwamitin da Victor Ndoma-Egba ta jagoranta kuma rahoton kungiyar da aka saki a 2007 ya same shi da laifin taimakon kansa da kudin Petroleum Training Development Fund (PTDF).
Sai dai Abubakar ya karyata hakan inda ya zargi Obasanjo da majalisar da yunkurin son hana shi zama shugaban kasa.
A kokarinsa na son ganin ya zamo shugaban kasa a zaben 2023 Atiku ya zamo jajirtaccen dan takara na PDP, kuma yana daga cikin yan gaba-gaba a yan takarar zabe mai zuwa wanda ake zatawa nasara.