Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban burinsa ga ‘ya’yansa shi ne ya tarbiyantar da su domin su kasance masu amfani ba wai ya bar musu abin duniya ba.
Ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin da ya kai gaisuwar Sallah ga Sarkin Daura Dr Faruk Umar Faruk, a fadarsa da ke birnin na Daura a Jihar Katsina da ke arewacin kasar.
“Abin da na fi mayar da hankali a kansa a ko da yaushe shi ne na tarbiyantar da ‘ya’yana yadda za su zama masu amfani duk inda suka samu kansu. Na gaya wa ‘ya’yana, musamman mata, cewa ba za su yi aure ba sai sun kammala karatun digirinsu na farko.
“Sun sani cewa ba zan bar musu gadon komai ba. Babban abin da zan bar musu shi ne na tabbatar cewa sun samu ingantaccen ilimi,” in ji shi.
Shugaba Buhari ya yi kira ga iyaye su bai wa ‘ya’yansu tarbiyya ta yadda za su kasance masu tsoron Allah da yin biyayya ga dokokin kasa da kuma yin rayuwa cikin ilimi.
“An daure ni tsawon fiye da shekaru uku bayan na yi shugabancin kasa. A wancan lokacin ne na fahimci [muhimmancin bai wa ‘ya’ya tarbiyya], kuma na shaida wa ‘ya’yana cewa babbar kadararku ita ce abin da ke kanku, ba abin da kuka mallaka ba,” a cewar Shugaban Najeriya.
Shugaba Buhari ya ce ya kamata a koaya wa matasa da kananan yara darasi kan tarihi, domin hakan zai sa su kasance masu kishin kasa da girmama manya.
Ya shaida wa Sarkin Daura cewa zai rika kai ziyara birnin a-kai-a-kai idan ya sauka daga mulki a shekarar 2023.
Daga BBC Hausa