Wata Mata Yar asalin Kasar Congo yace yanzu haka tana maraba da dukkan Namijin daya shirya Auren ta, Matar wacce yanzu haka take cika shekaru 70 a duniya.
Matar Mai suna Alphonsine Tawara, tace Maza da dama sun nemi Auren ta lokacin tana da kuruciya, Kuma tayi soyayyah mai tarin yawa sai dai a lokacin mata bukatar Aure.
Ta dauki hukuncin rashin yin Aure ne da wuri a kokarin ganin ta samarwa Yan’uwanta Karatu ingantacce.
Malamar Makaranta ce ta kwashe shekaru Mai tsawo tana karantar, bata da Yaro ko guda amma dalubanta suna kwashe mata kewar rashin Yaranta na Jini.
Yanzu haka tana neman Mijin Aure sai dai abun yana nema ya gagara, amma tana mai tabbatarwa da dukkan Wanda zai Aure ta zai same ta Sabuwa fil a leda kamar Budurwa.