• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Rikici Ya Barke Tsakanin Sheikh Bello Yabo Da Mallam Murtala Bello Sokoto Akan Yan Siyasa

ByLucky Murakami

Aug 9, 2022

A cikin wani bidiyo da mukai karo dashi cikin karatun Mallak Murtala Bello Sokoto yayi magana akan maganganu marasa dadi da Sheikh Bello Yabi yayi akansa inda shima ya mayar masa nasa martanin.

Inda ya fara da cewa zagi ba tarbiyar Annabi bace kuma ya karyata masu cewa Manzon Allah yana zagi a lokacin rayuwarsa, bayan an zagi shi Malam Murtala Bello. Inda yace yace wanda ya fara wannan zagi shine azzalumi kuma shi bazai rama ba.

Malam Murtala Bello Sokoto ya zargi maganar da yayi akan yan takarar shugaban kasa Bola Tinubu da Atiku Abubakar ce ta jawo masa wadannan zage zage.

Ya kuma kara da cewa tun daga shekarar 1999 zuwa 2019 tsohon malami ya nuna goyon bayansa ga wasu yan siyasa tun daga jihar sokoto har zuwa matakin shugaban kasa. Yaci mutuncin yan siyasa irinsu Attahiru Bafarawa, Alu Wammako, Aminu Waziri Tambuwal kuk saboda son abun duniya.

Ya kuma kara da cewa malamin yayi karya da yace ya yiwa Buhari kamfen a shekarar 2015 da 2019, inda yace malamin baiyi Buhari ba a lokacin.

Yace lokacin malamin yayima buhari kamfen shine a shekarar 2011 lokacin da yake kamfen da ayoyin bambancin musulmi da kafiri a matsayin shugaba.

Kazalika ya kuma kara da cewa a lokacin Jonathan anyi zargin shi malamin (Sheikh Bello Yabo Sokoto) da kasancewa cikin malaman da sukaci kudin kamfen.

Ga dai cikakaken bayani nan cikin bidiyon da zamu gabatar muku a kasa.

Bugu da kari a gaskiya wannan labari baiyi wa al’umma dadi ba ganin yadda malamai sukazo suna rikici a junansu. Wanda sune ya kamata a ce suna yiwa mutane nasiha akan irin wadannan abubuwa.

Muna rokon Allah ya zaunar mana da kasarmu lafiya.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

2 thoughts on “Rikici Ya Barke Tsakanin Sheikh Bello Yabo Da Mallam Murtala Bello Sokoto Akan Yan Siyasa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *