Bayan abinda ya faru da muka kawo muku Rikici Ya Barke Tsakanin Sheikh Bello Yabo Da Mallam Murtala Bello Sokoto Akan Yan Siyasa inda malam murtala bello sokoto yayi wa sheikh bello yabo martani inda yake cewa:
“Tun daga shekarar 1999 zuwa 2019 tsohon malami ya nuna goyon bayansa ga wasu yan siyasa tun daga jihar sokoto har zuwa matakin shugaban kasa. Yaci mutuncin yan siyasa irinsu Attahiru Bafarawa, Alu Wammako, Aminu Waziri Tambuwal kuk saboda son abun duniya.”
Kuma yace Sheikh Bello Yabo ya kira Bafarawa da dan shi’a, ya kuma kara da cewa malamin yayi karya da yace ya yiwa Buhari kamfen a shekarar 2015 da 2019, inda yace malamin baiyi Buhari ba a lokacin.
Yace lokacin malamin yayima buhari kamfen shine a shekarar 2011 lokacin da yake kamfen da ayoyin bambancin musulmi da kafiri a matsayin shugaba.
Kazalika ya kuma kara da cewa a lokacin Jonathan anyi zargin shi malamin (Sheikh Bello Yabo Sokoto) da kasancewa cikin malaman da sukaci kudin kamfen.
To a yau kuma mun kawo muku martanin da dalibin Sheikh Bello Yabo me suna Abubakar Malami wanda ya yiwa martanin nasa take “Wankin Dan Kanoma Tsakar Kasuwa.”
A cikin martanin da yayi ya farawa da cewa ba iya Sheikh Bello Yabo ne ya kira Bafarawa dan shi’a ba harda Mallam Musa Lukuwa wanda kowa yasan shi malami ne ga Mallam Murtala Bello. Yace yana da hujjojin da shi malamin yake fadar wannan magana domin yafi shekara 20 yana tare da malamin dan daukar karatu.
Ya kuma kara da cewa ya dade yana kokarin sulhunta Mallam Musa Ayuba dashi Sheikh Bello Yabo. Inda yake ta kokari akan hakan. Wanda yace har wasu malamai ya gayyato daga Gusau domin sulhunta su.
Sannan ya kara da rokon Sheikh Bello Yabo kada yasa baki cikin wannan magana domin shi zai wakilceshi.
Ga cikakken bidiyon nan ku kalla domin sauraran cikakken martanin da malamin yayi.
Bugu da kari malamin ya musanta malamin ganin yadda yace malam bello yabo yana bin yan siyasa don ya samu wani muqami ko kudi wajensu.
Ya Kuma tono gaskiyar inda shi Malam Murtala Bello ya fito, kuma ya qalubalance akan yace wasu daliban bello yabo yan shi’a ne. Yace duk abinda ya fada akan bellp yabo karya ne.
Ya kuma yi magana akan malamin yace shi baice a zabi Tinubu ba shima ya zayyano dalilai da suka tabbatar da hakan.
Kadan kenan daga cikin abubuwan da dalibin bello yabo fada a matsayin martani zuwa ga murtala bello sokoto.
Mai iska