• Wed. Feb 12th, 2025

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Sabuwar Hanyar Samun Bashin Bankin NIRSAL Cikin Sauki

ByLucky Murakami

Jul 11, 2022

Wannan sanarwar na zuwa ne a yayin da kasashen nahiyar Afirka da dama ke lalubo hanyoyin bunkasa harkar noma domin yalwar abinci a kasashensu.

Aliyu ya ce idan a kan harkar da ta shafi noma ne, hukumar za ta iya bayar da lamuni ga mutum daga Naira daya har Naira biliyan daya.

An kafa hukumar NIRSAL ce a shekara ta 2011 domin bayar da lamuni ga duk mai hada-hada da kuma zuba jari a cikin harkar noma.

“Abin da muke nufi da noma shi ne ba wai kawai shiga gona ko kiwon kaji ko kiwon dabbobi kadai ba, duk harkar da ta shafi noma da kiwo daga sarrafawa har zuwa sufuri da kuma sayarwa za mu ba su lamunin samun bashi a wajen bankuna ko kuma masu saka jari daga Naira daya har Naira Biliyan daya” in ji Aliyu Abdulhameed.

Shugaban hukumar ta NIRSAL ya kara da cewa idan banki ko mai saka jari ya saka kudinsa, idan aka samu asara hukumar NIRSAL za ta biya.

Matakan samun lamunin NIRSAL.

1. A rubuta wa daya daga cikin bankunan Najeriya takardar neman rance, sannan a nemi sahalewar hukumar NIRSAL domin lamuni.

2. Banki zai dubi takardar neman rancen, sannan ya aika wa hukumar NIRSAL dukkan takardu da ake bukata a madadin mai neman rance.

3. Hukumar NIRSAL za ta dubi takardun da banki ya mika mata sannan ta tabbatar da sahihancinsu da kuma cikarsu cif-cif.

4. Idan banki da kuma hukumar NIRSAL suka tabbatar da duk takardu sun cika, sai su ziyarci gona ko wurin kasuwancin mai neman lamunin.

5. Idan har hukumar da kuma banki suka aminta da ingancin harkar noma ko kiwo ko kuma kasuwancin da mutum ya shirya yi, sai NIRSAL ta bayar da lamuni ga mai neman rancen ta hannun banki.

6. Daga nan sai banki ya bai wa mutum kudin da ya nema rance domin fara sana’arsa, sannan ita kuma hukumar NIRSAL ta fara sanya ido kan yadda sana’ar ke gudana.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

3 thoughts on “Sabuwar Hanyar Samun Bashin Bankin NIRSAL Cikin Sauki”
  1. Assalam alaikum dafatan kunyin lafiya Allah yasahaka amin summa amin inada bukatar rancen kudi da zanyi kasuwanci ina saida wayoyi da kayan wayoyi ina zaune a garin kabomo karamar hukumar bakoro jahar katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *