Kamar yadda kuka sani Sadiya Gyale, wannan suna ne da ya jima yana yin tashe a cibiyar shirya Fima-fimai wacce aka fi da kira da, ‘Kannywood.’
Kamar sauran tamkar ta, Sadiya Gyale, ta daina fitowa a cikin shirye-shiryen Fima-fiman, bayan ta kwashe shekaru masu yawa da za a iya cewa kusan tun farkon kafuwar cibiyar shirya Fima-fiman ta Kannywood.
Ta yi zamanin da fuskanta mafiya yawan mutane ke son gani a cikin Fim din, masu shirya Fima-fiman da masu bayar da umurni duk ribibinta suke yi.
Kamar yadda masu sha’awan kallon Fima-fiman ke shaukin jin sunanta da kuma ganin fuskanta a cikin Fima-fiman.
To wace ce Sadiya Gyale, tana ina ne kuma a halin yanzun, bayan barin ta cibiyar shirya Fima-fiman ta Kannywood, me take yi ne a halin yanzun, wace shawara kuma take da ita ga ‘yan fim din na yanzun, musamman mata?
Duk amsoshin wadannan tambayoyin da ma wasun su suna cikin abin da za ku karanta a wannan hirar na ta kamar yadda jaridar Leadership Ayau ta rawaito.
A sha karatu lafiya: Muna so ki fada mana cikakken tarihin rayuwar ki?
Assalamu alaikum, kamar yanda ku ka sani, Suna na Sadiya Muhammad (gyale), an haife ni a Lagas ne, a watan Satumba shekarar 1985, iyayena duka Fulani ne, na yi karatun Firamare da Sakandare a Kano, na gama Sakandare a T/wadan Dankadai, na shigo’Industry,’ a shekarar 2003.
Alhamdulillah, mun yi lafiya mun gama lafiya, muna yi wa sauran fatan alheri.
Bayan kin bar fitowa a Fima-fimai, akwai wani aikin ko sana’an da ki ka koma yi ne, ko kuma makaranta ki ka koma?
Bayan na daina fitowa a Fima-fimai, ina sana’o’i kala-kala, na saye da sayarwa, da noma duk ina yi.
Mun ga kin samu shaidar yabo, ko za ki yi mana bayani kan yadda aka yi ki ka samu?
Wata kungiya ce ta makaranta Mujaallar fim, su ne suka karrama ni, da ma sun taba karrama ni, ban samu damar halarta ba.
Malama Sadiya, ya ya batun aure, yaushe za ki kara kiran mu mu rakashe?
Insha Allah muna ta addu’a, Allah Ya kawo miji nagari mafi alheri.
Ko Kina da sha’awan zama mai bayar da umurni ko mai daukan nauyin shirya Fima-fiman ne, na kanki bayan kin yi aure?
Daman can nakan dauki nauyin shirya Fima-fiman, kuma ko na yi aure ma zan ci gaba da hakan.
Ta ya ya aka yi ki ka samo lakabin sunan “Gyale”?
Na samo sunan gyale ne a fim din gyale, fim din gyale shi ne fim di na na farko, wanda na fara yi, wannan ne ya sa ake kira na da Sadiya gyale.
Kin yi fima-fimai da dama, wanne ya fi kwanta ma ki a rai?
Akwai fima-fiman da suka kwanta min a raina sosai, kuma ina alfahari da su irin su, Gyale, Sanafahana, Kugiya, Armala, Gudun kaddara da dai sauransu.
Wane fim ne ya fi ba ki wahalar yi?
Fima-fiman din da suka ba ni wahala suna da dan yawa.
Ko akwai wani ‘role’ da aka taba ba ki a fim ki ka ki karba ki hau?
Ehh, akwai wadanda na ki karba saboda wasu dalilai.
Ko akwai wata jarumar fim da ta zama abar koyi gare ki a duniyar fim (Indiya, Amurka, China ko fima-fiman kudanci)?
Babu ita, ba wata jaruma da nake koyi da ita.
Wane fim ne na karshe da ki ka yi?
Ba zan iya tuna sunan fim din da na yi na karshe ba, amma na san fim din Falalu dorayi ne.
Ko akwai furodusa da daraktan da ki ka fi son yin aiki da su?
Ehh, akwai su da yawa, ba za su lissafu ba, wadanda nake jin dadin aiki da su.
Me ya sa?
Kila saboda haduwar jinni ne.
A ganinki wasu abubuwa ne suka sauya a masana’antar fim a yanzu, idan aka kwatanta da lokacin ku?
Abubuwa da yawa muna samun labarin sun sauya, amma tun da ba cikin harkar nake ba yanzu ba zan iya cewa komai ba.
Su wane ne gwanayen ki a fagen fim?
Gwanaye na suna da yawa mata da maza, wadanda su ke burgeni.
Wace shawara za ki baiwa ‘yan mata masu shiga fim a yanzu da masu sha’awan shiga?
Ina masu fatan alheri, kuma ina ba su shawara da su rike sana’ar fim, don mu har gobe muna ganin amfanin ta,
muna kuma cin albarkacin ta. Allah Ya karawa wannan sana’a albarka da daukaka ina alfahari da ita.
Ko za ki fada mana wasu irin saye da sayarwan ki ke yi, da kuma fima-fimai nawa ki ka dauki nauyin shiryawa?
Abubuwa ne da yawa, kayan yara, kayan maza da na mata, har da kayan noma da noman kan shi.
Yanzu idan aka kira ki, don ki fito a fim, za ki karba ki je ki yi ?
To ya danganta da irin fim din da zan iya fitowa ne a halin yanzu.
Mun gode da lokacin da ki ka ba mu.
Ni ma na gode.