Sarkin Daura ya sake yin wuff da budurwa mai shekaru 22, hotuna sun bayyana.
Labari mai zafi da amihad.com ke tattaro muku shi ne na yadda Sarkin Daura, Alhaji Dr. Umar Faruk ya sake yin wuff da budurwa danya shakaf mai shekaru 22 a duniya.
Kamar yadda @fashionseriesng suka bayyana, an yi bikin ne ba tare da wata hayaniya ba a makon da ya gabata.
Zukekiyar amaryar mai suna Aisha Gona Safana ta tabbata sabuwar gimbiya a Daura.
A shekara 90, Sarkin Daura ya auri tsaleliyar Amarya ‘yar shekara 20 A wani labari na daban, Daily Nigerian na ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.
An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano.
Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.