A safiyar yau amihad.com ta samu labarin dambarwar ma’aurata wanda ya kasance bayan sati biyu da yin auren wasu masoya matar ta bukaci sai mijin nata ya saketa saboda baya iya gamsar da ita a kan gado.
Wannan ba sabon abu bane a wannan lokaci ganin yadda abubuwa makamantan haka suke faruwa tsakanin ma’aurata. Kuma abun mamakin shine amfi samun irin wannan matsala ta bangaren maza.
Kamar yadda kuka sani a zaman takewar aure ana yawan samin matsaloli tsakanin mata da miji wajan gamsar da juna, shi yasa wani lokacin zakuga aure yana yawan mutuwa.
Binciken amihad.com ya tabbartar mana da cewa, da yawa daga cikin ma’aurata daga Maza har Mata basusan abubuwan da ake da ake kafin gudanar da jima’a ba musamman ma ga Namiji, wanda dole shi yakamata yasan wadannan abubuwan domin sai mayarsa tafi ganin daukar sa cikakken Namiji.
Domin kuwa duk Namijin da baya iya gamdar da matarsa to tabbas watarana za’a wayi gari ta renashi domin gamsar da mace yana daya daga cikin abin da zatana kimanta Namiji, wanda ma bazata yarda ku rabu ba.
Sai a yau kuma muka sami wani labari abin mamaki ga wasu ma’aurata wanda duka-duka auren nasu bai wuce makwanni biyu 2 ba, amma matar take cewa sai ta rabu da mijin nata.
Matar ta kai korafin mijin nata akan baya gamsar da ita domin wasu abubuwan ma sai ita take koya masa ko kuma tanayi da kanta ma yayin da suke jima’a, wanda auren nasu bai wuce sati biyu 2 ba.
A cikin wasu hotunan tsokaci da mijin nata yake a kafafan sada zumunta yadda yake zargin matar tasa tana cin amanarsa ko kuma kafin suyi auren dama tasan Namiji.
A cikin korafin da mijin nata yake yana nuna cewa matar tasa tana masa korafi akan cewa baya gamsar da ita lokacin da suke jima’a.
Sannan kuma ya kara da cewa: Matar tasa tana kirkirar wasu salo-salo na kwanciya aure wanda shi kansa bai san dasu ba, kuma bai taba jin labarin ana irin wannan kwanciyar ba amma sai yaga matarsa tana yi masa.
Ga dai bayanin da ya wallafa cikin harshen turanci, inda bayaninsa ya fara kamar haka;
“Salamualaikum, pls i need advice on this before i start seeing things that are not there. I got married to my cousin 2 WEEKS AGO. We haveloved eachother ever since we werelittle.”
Sannan ya kara da cewa:
“We dated for about 5years before we got married. From those 2 weeks till now, she has been complaining that i don’t satisfy her as a husband. She initiates styles and method i have ever imagined and still complains that i don’t lastlong in bed. Ni gaskiya na fara zargin ta…I know we are cousins and have known eachother for long, but even while dating we never talked about intimacy indept, just a few out of curiosity and even that.”
A cikin jawabin dayake dai ya nuna cewa matar tasa yar uwarsa ce, kuma sunyi soyayya tsawon shekara biyar.
Shawarar da amihad.com zata bayar daga karshe itace ya kamata ma’auta su fuskanci junansu akan irin wadannan matsaloli domin neman mafita ga matsalar bawai su fito da abu cikin jama’a kowa yazo yana ji ba.
Muna fatan Allah ya kara rufa mana asirin kuma ya kare mu daga irin matsaloli da suke kawo karshen aure.