• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Saura Kiris Na Zama Biloniya Da Harkar Kirfto Amma Cikin Minti 5 Nayi Asarar Komai

ByLucky Murakami

Aug 21, 2022

Wani dan kasuwar kirifto ya fadi yadda ya kai rabin hanyar zuwa zama hamshakin attajirin da ke saka hannun jari a cryptocurrency amma yayi asarar komai cikin mintuna biyar kacal.

Ya ce ya rasa komai lokacin da darajar kudin ya fadi kuma aka bar asusunsa da $0 kafin ya iya yin komai.

Ya kuma bayyana cewa ba zai iya bayyana kansa ba saboda tsoron kada a yi masa ba’a saboda an gargade shi da saka hannun jari a cikin kudin daya saka a kasuwar kirfto.

Kamar yadda jaridar Legit.ng ta rawaito, wani mai saka hannun jari na cryptocurrency ya ba da labarin yadda ya sake zama matalauci a cikin ƙasa da mintuna 5 da zama mai arziki.

Yayi amfani da shahararren shafin sada zumunta na Reddit wanda ba’a bayyana sunansa ba ya yi iƙirarin cewa ya sami dala miliyan 1.3 (N532.97 biliyan) bayan ya saka hannun jari a kasuwar SQUID QAME, kuɗin sulalla da aka yi shi da sunan wani shiri da yayi kaurin suna a shafin Netflix me suna Squid Game.

Amma bayan ganin darajarsa ta haura sama da dala miliyan 2 a cikin walƙiya darajar tsabar kudin ta ragu zuwa $0.

Squid Game Coin a watan Nuwamba ya haura zuwa babban farashin $2,681 kafin ya fadi zuwa $0.01 faɗuwar kashi 99.99 cikin ƙasa da wata guda.

kamar yadda binciken amihad.com ya tabbatar akwai rahotanni da yawa cewa yanayin yadda aka gudanar da kasuwancin wannan kudin kirifto na iya zama zamba, wanda akafi sani da “rug pull” a kasuwar kirifto.

Wanda kuma hakan na faruwa ne lokacin da wanda suka kirkiro aikin suka fitar da tsabar kuɗin da yake cikin kasuwar suka ba iya koyin din.

Mutumin yace ya kasance mai sha’awar shiga harkar kasuwancin kuma yana son saka hannun jari a Squid Game bayan yayi bincike.

Yace:

“Na yi tunani, bari in saka $10 (N4000) a cikin wannan kawai don nishaɗi. Na sami kusan SQUID 661. Yayin da kwanaki suka wuce, na fara ganin yana hawa, 1$, 2$, 5$, 10$, 30$.” kuma ina tunani.. Yayin da nayi tunanin ko zan iya fitar da kudin nan.

“Tabbas, na san cewa ba zan taba fitar da kudin ba, na gamsu da hakan, amma abin farin ciki ne ganin hakan ya faru.”

Mutumin ya ce bayan kwana biyu farashin SQUID ya tashi zuwa dala 2,000, wanda hakan ke nufin zai samu sama da dala miliyan 1.3.

Sai dai bayan mintuna biyar tsabar kudin ta fado babu komai kuma ya rasa komai.

“Yanzu zan iya cewa ni hamshakin attajiri ne a wani lokaci na rayuwata”

Dan kasuwar ya kammala da cewa ya kasance yana sane da wannan zamba kuma ya shawarci sauran masu zuba jari kada su taba “sanya kudi akan tsabar kudi, ko da yaushe yin bincikenku kuma ku yi hankali kan abin da kuke zuba jari.”

Ya ba da shawara:

Rashin ikon canza kudin sulalla zuwa kudin zahiri cikin lokaci na ɗaya daga cikin manyan haɗarin saka hannun jari a kirifto. Za ku iya dawo da kuɗi idan akwai buƙata, don haka kuna iya rasa duk kuɗin ku.

Idan darajar ta faɗi zuwa sifili, ko dai saboda zamba ko kuma saboda masu saka hannun jari sun rasa kwarin gwiwa, za a iya barin ku riƙe tsabar kuɗi na sulalla mara amfani waɗanda ba za ku iya siyarwa ba.

Sabbin kudin sulalla da aka kirkira sun fi haɗari fiye da waɗanda aka kafa kamar Bitcoin da Ethereum – ba kaɗan ba saboda akwai haɗarin zamba.

A halin da ake ciki, wanda suka saka hannun jari na Bitcoin sun ga sama da Naira tiriliyan 1 sun sauka cikin jarin su yayin da kasuwar kirifto ta fadi a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *