• Thu. May 23rd, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Sheikh Daurawa Ya Bayyana Abinda Ummita Ta Fada Masa Kafin Saurayinta Dan China Ya Kasheta

ByLucky Murakami

Sep 19, 2022

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cikakken bayanin magana ta tsawon mintuna 15 da su ka yi da marigayiya Ummakulsum Buhari (Ummita) ta wayar tarho game da saurayinta, mako guda kafin rasuwar ta kamar yadda majiyarmu jaridar Daily Nigerian ta rawaito.

 

Wani ɗan kasar China, mai suna Gheng Quanrong ne ya hallaka Ummita, bayan da ya caccaka mata wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano.

Da yake bayyana abinda su ka tattauna da marigayiyar a wani faifen bidiyo ds ke nuni da cewa a ɗaya daga cikin majalisin karatunsa ne, Daurawa ya ce ta kira shi ne domin neman shawara a kan mafita kan ƙudurin 5a na aurar ɗan China ɗin sabo da mahaifanta sun hana ta auren shi.

“Na ce mata iyayenki su na da gaskiya saboda bai kamata nata ku riƙa auren wanda a ke da kokwanto a kan asalinsa,” in ji shi.

Sai dai malamin ya ce ya bata shawarar ta gindaya wa masoyin na ta sharɗɗa biyar kafin su yi auren.

“Sharadi na farko shi ne a tuntubi hukumar shige da fice ta ƙasa don tabbatar da ko da izini ya shigo ƙasar nan. Na biyu, a yi bincike kan aikin sa a Najeriya.

“Na uku, na san Sarkin Kano ya naɗa sarkin ƴan China a Kano. Don haka a tambayi shugaban al’ummar kasar ko sun san shi, yankin da ya fito da kuma abin da yake yi?

“Na huɗu, ya kamata kuma a sanar da ofishin jakadancin cewa ɗan kasar China na shirin auren ƴar Najeriya. Na biyar kuma na umarce ta da ta sanar da Hisbah don ta kara koya masa addinin musulunci, tunda ta ce min ya musulunta.

“Ummita ta kara da cewa iyayensa a kasar China sun amince da auren, amma iyayenta sun ki amincewa da auren.

“Amma na gaya mata idan kun cika waɗannan sharuɗɗa guda biyar, zan shawo kan iyayenki su yarda ki aure shi,” in ji shi.

Daurawa ya ƙara da cewa addinin Musulunci ya amince da auren jinsi, yana mai cewa addinin ya kyamaci nuna wariyar launin fata, inda ya ƙara da cewa marigayiyar ta faɗa masa cewa ɗan China ɗin ya musulunta.

Sheikh Daurawa ya kuma yi kira ga hukumomin da su ke da ruwa da tsaki da su tabbatar an hukunta ɗan China da ya kashe Ummita.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *