• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Shin Da Gaske Ne Shugaba Buhari Ya Saida NNPC Ga Yan Kasauwa?

ByLucky Murakami

Jul 20, 2022

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da kamfanin mai na kasa wato NNPC, wanda a ka sauya wa riko a yanzu ya koma kamfanin ‘yan kasuwa mai zaman kansa.

Bikin kaddamarwar wanda ya gudana a yau Talata a Abuja, wanda aka yi masa lakabi da”mai dimbin tarihi”.
Kamar yadda ya bayyana a jawabin sa an mayar da ikon gudanar na kamfanin mai naNNPC ga ‘yan kasuwa, saboda a inganta shi, domin samar wa kasa abubuwan da ta ke bukata.

Ga jawabin kamar haka:

”Daga yanzu kamfanin Mai na NNPC ya koma karkashin ikon ‘yan kasuwa, zai kasance kamfani mai zaman kansa ta yadda zai hada sahu da sauran takwarorinsa a fadin duniya, domin ganin an ci gaba da bunkasa hannayen jari sama da miliyan 200 tare da habaka fannin mai a fadin duniya.

A yanzu haka doka ta dora wa kamfanin alhakin tabbatar da samar wa Najeriya wadataccen mai, domin samun habakar tattalin arziki ta hanyar farfado da wasu fannonin da ke bukatar mai” in ji Buhari.

A wani labarin kuma Wani babban jigo a jam’iyyar APC a jihar Edo, John Mayaki, ya ɗora alhakin shan kashin da jam’iyyar tayi a zaɓen gwamnan jihar Osun akan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana naƙasun shugaba Buhari

Da yake magana akan shan kashin da jam’iyyar tayi, Mayaki ya zargi shugaba Buhari da nuna halin ko in kula da kuma yarda da yayi wasu ƴan jam’iyya na aiki domin ganin bayan ta. Jaridar Daily Trust ta rahoto.

Yace idan har ba shugaba Buhari ya sauya salon sa na yin biris da lamuran da suka shafi jam’iyya ba, hakan na iya kawo naƙasu ga jam’iyyar a zaɓen 2023.

Rashin tsoma bakin da shugaban ƙasa yake abu ne mai kyau ga dimokuraɗiyyar ƙasar nan amma hakan ba uzuri bane akan watsi da nauyin dake kansa a matsayin shugaban jam’iyya wanda yakamata ace yana sasanta ƴaƴanta, tabbatar da biyayya da kuma ƙara mata ƙarfin ikon siyasa.

Boren da wasu manyan ƴaƴan jam’iyyar APC, gwamnoni da ministoci a ƙarƙashin gwamnatin Buhari ke yi, shine abinda yasa jam’iyyar ta sha kashi a zaɓukan jihohin Edo da Osun.

A ƙarƙashin shugaba Buhari, gwamnonin APC sun yi aiki domin faɗuwar jam’iyyar a jihar Edo, haka ma an nuna yatsa ga wasu ƙusoshi cikin gwamnatin sa kan faɗuwar da jam’iyyar tayi a jihar Osun.

Sai dai shugaban ƙasa ba zai yi ko da kashedi ga waɗannan masu lalatar jam’iyyar ba, hasalima yana nuna yarda da hakan wanda yake ƙara musu ƙarfin cigaba da yin abubuwan da suke yi. Ya faɗa a cikin wata sanarwa.

Ya shawarci ƴaƴan jam’iyyar na jihar Osun

Ya ƙarawa ƴaƴan jam’iyyar na jihar Osun ƙarfin guiwar kan su koya daga darussan da suka samu a shan kashin da jam’iyyar tayi sannan suyi aiki tuƙuru wurin ganin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa.

Ya shawarci shugaba Buhari akan ya koyi yadda ake shugabancin jam’iyya daga wurin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *