Family & Relationships

Soyayya Da Rayuwar Aure: Matakai 7 Dake Sa Dorewar Aure Har Zuwa Tsufa Ko Mutuwa

Idan har kana shirin yin aurene, to akwai wasu muhimman matakai da ya kamata ka sani, kuma ka shirya masu kafin zuwan wannan rana. Idan kuma har ka riga da kayi auren, to watakil ka fahimci cewa zamantakewar aure ba karamun abu bane.

1. Sadarwa

Ga dukkanin mutane biyu da ke son kulla kyakkyawar zamantakewar aure, amfanin sadarwa a tsakaninsu baya misaltuwa. Da yawan zamantakewa na lalacewa ne sakamakon katsewar sadarwa ko daina sadarwar gaba daya.

Domin bunkasa sadarwa tsakaninka da abokin zamantakewarka, yana da kyau ka fara fahimtar irin zantuka da tattaunawar da yake so kuna yi tare. Karka kasance mai bijiro da zantukan da sam baya sonsu, hakan ne zai sa sadarwarku ta dore.

2. Baiwa juna tazarar lokacin kadaita

Dabarar baiwa juna tazarar lokacin kadaita naiya zamowa banbarkwai ga jama’a. Amma, ga mafi yawan mutane, suna bukatar wasu lokuta na kansu, don kebewa ba tare da takura daga wani ba, koda kuwa abokin zamantakewarsu ne na aure.
Domin cimma wannan, ka shirya wasu ranaku da zaka baiwa abokin

zamantakewarka damar fita shakatawa da ‘yan uwansa ko kawayensa. Zaka sha mamakin irin kuzari da nishadin da zai dawo gida dashi.

3. Ka karfafa Yarda a tsakaninku

Yarda itace ginshiki na kowacce zamantakewa ta rayuwa musamman a zamantakewar aure. Da yawan mutane na ganin cewa ma damar babu yarda, to babu amfanin ci gaba da zamantakewa. Tabbas, yarda ginshiki ce da bai kamata ayi wasa da ita ba.

Ana gna yarda ne a cikin dogon lokaci, amma akan iya rusata a cikindakiku kadan. Da wannan yake da kyau kowannenku yasan iyakar mu’amalar dan uwansa, ta yadda wani ba zai shiga gonar wani ba.

Idan kuna a shafi daya; to akwai saukin gane halayyen juna da kuma kulla yarda mai dorewa.

4. Grimama juna

Girmama abokin zamantakewarka ya zama wajibi. Rashin girmama na gaba da kai kan iya jefa zamantakewarku cikin tsaka mai wuya, ko kuma kawo karshen zamantakewar gaba daya.

Girmamawa kusan itace ta gina kowanne dan Adam. Don haka, zamantakewar aure tana bukatar ma’auarata su kasance masu girmama junansu. Da sanin girman junane ake taka tsantsan a lokacin da ake wata husuma don kar a wuce gona da iri.

5. Samun lokutan na musamman tare da juna

Musayar kyawawan kalamai a lokacin da ake karin kumallon safe tsakaninka da abokin zamanka, ya zarce awannin da kake shafewa kana kallon talabijin ko karanta jarida a kusa da abokin zamanka.

Samun lokuta na musamman don kasancewa tare da junanku na da muhimmanci a zamantakewarku. A duk lokacin da ka baiwa wani mutum wani bangare na lokacinka, ka nuna masa cewa ka damu da shi.

Don haka duk lokacin da ka dawo daa wajen aiki, ka kokarta zama tare da abokin zamantakewarka don tattauna batutuwan rayuwar yau da kullum. Hakan zai taimaka wajen kara karfafa dankon soyayyar dake tsakaninku.

6. Soyayya

Soyayya kusan ita ce makasudin da yawancin mutane ke yarda da juna har suyi aure. Soyayya na sanya mutane aikata wasu abubuwan masu ban mamaki kuma soyayya ce ke sanya mutane kasancewa da junansu ba tare da duba banbancin da ke tsakaninsu ba.

Sai dai, kamar komai na wannan duniyar, shima SO zai iya shafewa idan lokaci na tafiya, don haka akwai bukatar bullo da dabarun ci gaba da zama tare koda soyayyar na raguwa.

Zaka yi matukar mamaki idan ka gane tasirin aika sakon kartakwana na “Ina sonka/Ki”, wannan sakon na iya sanya abokin zamanka yin tsalle cike da murna.

7. Hakuri da saurin canja Ra’ayi

Idan har ka shirya yin aure, kuma kana tunanin cewa komai zai faru a gidanka a yara kake so ba tare da ka canja ra’ayi ba, to don Allah ka sake tunani.

Babu wata zamantakewa da ta cika kashi 100 kma hakan yasa dole ma’aurata su kasance masu hakuri da junasu da kuma yin yafiya a lokuta da dama.

Tabbas ba lallai bane ka samu duk abunda kakeso a kowanne lokaci kake sonsa. Don haka, wasu lokutan dole ka yi hakuri da wanda ka samu, ka zamo mai sassauci ga abokin zamanka.

Aure rayuwar zaman jin dadi da batawa juna raice, don haka dole hakurine zai iya rike ku tare na tsawon lokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button