• Wed. Feb 12th, 2025

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Subahanallahi! An Sace Amarya Da Ango Ana Tsaka Da Shagalin Biki A Katsina

ByLucky Murakami

Aug 8, 2022

Labarin dayake shigo mana a safiyar yau shine yan bindiga sun sace amarya da ango ana tsakiyar shagalin bikinsu.

Mun samu rahoton kamar haka:

Innalillahi Yan Bindiga Sun Sace Amarya da Ango A Garin Katsina Ana Tsaka’da Shagali Qalu Innalillahi Wannan Lamari Yayi Muni.

BBC ya ruwaito mazauna unguwar na cewa ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 1 da minti 25 na daren Asabar, inda suka shafe tsawon sa’a guda su na harbe-harbe.
Sun shaida cewa ’yan sa-kai sun rasa rayukansu ne a kokarin hana garkuwa da ma’auranta, sannan an jikkata wasu daga cikinsu.

Rahotanni na cewa dole ta sanya masu aikin sa-kai janye jiki bayan sun fahimci cewa ’yan bindigar sun fi karfinsu.

Wani mazaunin unguwar ta Shola da ke cikin Katsina ya shaida wa BBCn cewa, ’yan bindigar sun shiga unguwar ne bisa babura dauke da bindigogi suna harbe-harbe.

Mutumin ya ce ’yan bindigar sun fasa wani gida ta baya suka shiga, lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da jikkatar wasu biyun.

Ya kuma ce baya ga sabbin ma’auratan akwai mutane da dama da aka sace, sai dai bai san adadi ba.

Wannan dai ba shi ne karon farko da mahara ke aukawa unguwar Shola ba, ko fiye da wata guda ma ’yan bindiga sun shiga yankin.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar wannan hari, inda ya ce jami’ansu sun dukufa don kubutar da amarya da angon.

SP Gambo ya kuma ce sun kubutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a kauyen Tandama cikin Karamar Hukumar Danja, bayan wani samame da suka kai maboyar ’yan bidiga.

Kazalika, ya ce a yankin Karamar Hukumar Safana ma, sun yi nasarar kashe wani kasurgumin dan fashin daji mai suna Albdulkarim Faca-Faca da mutanansa bakwai a karshen mako, bayan barin wutar da wani jirgin yaki ya yi akan maboyarsu.

Yan Bindiga Sun Sace Amarya da Angon Ta Ana Tsaka’da Shan Shagalin Bikin Su Babu Tausayi a Zuka’tan Su Yanzu Haka Muna Tafeda Bidiyon Da Zai’yi Matukar Tabbatar Muku da Hakan Zamusa Muku Shi Domin Kuji Cikakken Rahoton.

Wannan Kenan kadan Daga Rahoton Mu Akan Wannan Lamari Na” Sace Amarya da Angon ta da akai a Jahar Katsina.

‘Yan Bindiga sun cimma cikin Birnin Katsina

Cikin Sati Biyu kacal ‘Yan Bindiga sun kai Hari Hudu jere a ciki da gefen Birnin Katsina, sun kai Hari Kauyen Na Tsinta Bayan Babban Bakirin Katsina sun Kashe Mutane sun Saci wasu, san nan sun kai Hari Kauyan Ɗan Tsauni Bayan Asibitin Babbar Ruga sun Kashe Manoma sunyi Garkuwa da Mutane masu Yawa.

Ana cikin wannnan Firgici da Tashin Hankali Daren Jiya Asabar 6 ga Watan Ogusta Mutunen dake Rayuwa Cikin Unguwar ‘Shola Quarter’s’ da ke cikin Birnir Katsina suka tsintsi kansu cikin Tashin Hankali cikin Daren bayan sun ji Karar Harbe-Harben Bindiga babu Saurarawa.

“Yan Bindigar sun yi Barna sosan gaske, domin sun Sace Amarya da Ango kanan sun kashe Ɗan Sintira ɗaya sun Raunata Mutane Biyu ba a san iya adadin Mutunen da suka Sace ba Bayan Ango Da Amarya.

Zuwa haɗa wannan Rahoto Mutunen Unguwar suna ta Hijira domin samun Mafaka daga Waɗannan ‘Yan Ta’adda. Rundunar ‘Yan Sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin Kakakin Rundunar ASP Gambo Isa.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *