AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    Home » Sura Da Siffofin Uwa Ta Gari
    Family & Relationships

    Sura Da Siffofin Uwa Ta Gari

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiAugust 17, 2022No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email
    Share
    Facebook Twitter LinkedIn WhatsApp Pinterest Email

    Akwai abubuwa da dama a ake dubawa wajen gane wacece uwa ta gari to inganta tarbiya da dadin zaman aure.

    Gasu daga cikin wadannan siffofi zamu tattauna:

    LALLE

    Yar’uwata ki sani lalle kwalliyace ga duk ya mace kuma mace idan tabar hannunta ko kafarta ba lalle to ba’a iya banbance ta da namiji.

    Kuma kowace irin kalan lalle da mata sukeyi kema kiyi da zaran ya goge sa ki biyoshi da wani kala domin cika siffarki ta ya mace.

    BANGAREN ADO

    Yar uwa ki sani kirkire kirkiren adon zamani wajibine akanki a gidan mijinki harma da irin naki salon adon, kuma duk wata dressing da mata sukeyi a duniya dolene ki rinka yiwa mijinki matukar bai sabawa addinin musulunci ba, sannan kiyi masa ado da duk irin kayan da kika mallaka.

    KISISINA DA KARERAYA

    Ya yar’uwata mace bata cika mace ba idan bata iya kisisina irin ta mata ba, kamar su kareraya, yanga da rigima. Kuma ki sani irin wadannan dabi’un su suke daukaka martabar mace a wurin mijinta acikin dukkan alamuran su, Magana ko tafiya ko kallo da makamantansu.

    DAMUWA DA DAMUWARSA

    Yar uwa wajibine ki karanci halin mijinki sosai kisan mijinki acikin halin farin ciki da kuma bakin ciki kuma ki lura da yanayin sa a lokuta kamar haka:

    • Lokacin fita nema
    • Lokacin dawowa daga nema
    • Lokacin gajiya
    • Lokacin farin ciki
    • Lokacin bakin ciki
    1. LOKACIN FITA NEMA:

    A wannanl okaci yaruwata ki sani dolene ki tabbata mijinki ya fita daga gida cikin kwanciyan hankali da natsuwa.

    Akwai wani dabi’a da matan magabata sukeyiwa mazajensu, su kan shirya bayan sunyi wanka da kwalliya sannan sai su raka mazan su har kofar gida ko kofar dak.,

    Sannan suna tafiya suna taku daddaya da rangwadi kuma su kan yimusu addu’a sannan su basu wasiyan cewa idan Allah yasa ka samu halal ka kawo mana, idan kuwa baka samu ba zamuyi hakuri da azabar yunwa akan azabar Allah.

    Bayan ya fita yayi nisa sai ki kirashi da wani sunan soyayya mai dadi sai kiyi masa Kiss da hannunki. Sai kice masa Allah ya bada sa’a. Allah ya sa mudace Ameen.

    2. LOKACIN DAWOWA DAGA NEMA:

    Kisani yar’uwata miji yana dawowa gida a halin gajiya kafin ya dawo kin shirya ma dawowarsa.

    3. LOKACIN GAJIYA:

    A wanna lokaci ki sani zaki nemi ruwa mai dumi a lokacin sanyi idan kuma lokacin zafine, sai kinemo ruwan sanyi ki kai masa wurin wanka bayan ya gama wankan ya dawo daki ki bashi abinci.

    4. LOKACIN FARIN CIKI:

    Yar’uwata a wannan lokacine zaki baje kolin shagwabar ki da rungumarsa

    5. LOKACIN BAKINCIKI:

    Yar’uwata a wannan hali babu wasa babu tsokana a tsakaninku har sai kinji mai ya bata masa rai, idan ya fita bai samo bane sai ki kwantar masa da hankali, sai ki nuna masa kullum Allah yana basa sai kawai don yau baka samo ba sai muyi hakuri mu godewa Allah.

    Idan kuwa wani ne ya bata masa rai, sai ki bashi hakuri da kuma kwantar masa da hankali, sannan idan ya dawo miki cikin tashin hankali sai ki warware masa bayan kinji mai ya faru dashi.

    Idan ba zaki iya warware masa ba sai ki kaishi inda za’a warware masa damuwarsa.

    IYA ABINCHI

    Rashida wallahi wannan shine babban hanyar sace zuciyar miji idan har kin iya abinci sosai, wallahi sai dai kiji mijinki yana cin abinci yana santi yana kuma cewa amarya Allah ya miki Albarka harma ya miki kyauta sakamakon santin cin abincin.

    Sannan ba zai taba jin tsoron duk bakon da akayi ba ta bangaren abinci kam ko da kinyi masa laifi sai yace ya yafe saboda santin abincin.

    Ma'aurata Rayuwar Aure Soyayya
    Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr WhatsApp Email

    Related Posts

    Yadda Kanin Miji Ya Dirkawa Amaryar Yayansa Ciki A Nasarawa

    November 19, 2022

    Sati Biyu Kacal Da Yin Aure Amarya Ta Bukaci Ango Ya Saketa Saboda Baya Iya Gamsar Da Ita A Kan Gado

    November 18, 2022

    Yadda Ake Kwalliyar Maida Tsohuwa Yarinya

    November 7, 2022

    Lokuta Da Yawa Maza Yan Iska Sunfi Iya Soyayya Wata Budurwa Ta Kira Ruwa

    November 5, 2022

    Yadda Ango Yayi Dawowar Bazata Ya Kama Matarsa Da Babban Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    November 4, 2022

    Bidiyon Hira Da Matar Da Take Auren Maza Biyu Kuma Suke Kwana Kan Gado Daya

    November 3, 2022
    Add A Comment

    Leave A Reply Cancel Reply

    Check Also

    Ya Kamata Kusan Da Wadannan Tsaruka Na Tallafi Da Ake Bawa Yan Nigeria

    January 27, 2023

    FG Begins SMEDAN ₦1.5m Loan – Application Portal

    January 20, 2023

    How to Obtain an Ecowas ePassport as a Holder of a Nigerian Passport

    January 20, 2023

    Easy Way to Apply for a Visa in Nigeria

    January 20, 2023

    Apply 2023 Microfinance Bank Kaduna Recruitment

    January 20, 2023
    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2023 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.