Dubun wani magidanci dake lalata da matar makwabcinsa ta cika yayin da aka kamashi turmi da tabarya akan matar makwabcin nasa a Otal kuma aka daukesu hotuna dan tabbatar da faruwar Lamarin.
Sannan ita kuma matar makwabcin nasa an bayyanata da sunan Mai Prince wadda tace bata san shi bane dan ya mata maganane a Whatsapp ba tarr da hoto ba, sai bayan data tura mai hotunanta tsirara sannan ta ganeshi.
Tace bata san yanda aka yi har lamarin ya kai ga haka ba.
Shima Fundu ya bayar da ba’asin cewa bai san Mai Prince matar aure bace dan ta gayamai cewa sun rabu da mijinta.
Wannan lamari ya farune a kasar Zimbabwe inda wanda aka kama din aka bayyanashi da sunan Sheunesu Fundu wanda kwararren Kawune dake aiki da wata kungiya me kare hakkin yara mata.