Cikin bidiyon hira da akayi da babban jarumin Kannywood Tahir Fagge yayi bayani akan wasu sirruka da suka shafi rayuwarsa.
An tambayeshi dalilin dayasa yake zuwa gidan gala yake rawa da yan matan bidiyo kala-kala sunata yawo a shafukan sada zumunta.
Sai dai abinda akaji daga bakin jarumin shine ya tabbatar da irin alkairin da yan gidan gala sukai masa wanda hakan ne yasa shima yaje don ya taimaka musu saboda halin da ya shiga.
Ashe dai ciwon zuciya ya hadu dashi wanda kuma bashi da kudin dazai yiwa kansa wannan maganin duk cikin kannywood a rasa wanda zai dauki kudi ya taimaka masa sai yan gidan hala ne suke kawo masa dauki wanda shine shima ya saka musu da wannan abu.
Sai dai cikin bidiyon hirar da akai dashi ya fito fili ya bayyana sunayen jaruman Kannywood wanda suka taimaka masa cikinsu shine Ali Nuhu wanda ya saya masa sabuwar waya kafin kwantawarsa rashin lafiya wanda a karshe ya saida wayar yasa kudin cikin jadawalin siyan magani kamar yadda amihad.com ta tabbatar.
Kazalika ya bayyana sunaye wanda yace Rarara ya bashi dubu ashirin
, Maishadda ya bashi dubu ashirin, Abdulamart ya bashi dubu shabiyar. Sai kuma amihad.com ta gano sauran Jarumai wanda ya bayyana suanyensu wanda suka hada da Aisha Humaira da Daddy Hikima (Abale).
Ga wani sharhi da Tashar Tsakar Gida tayi a Youtube sai ku kalla kuji cikakken bayani.
Kamar yadda yace bashi da kowa sai Allah a cikin hirar da akayi dashi, muna rokon Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira.