• Sat. Oct 12th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Talakawa Ba Za Su Shiga Aljanna Ba – Inji Wani Minista

ByLucky Murakami

Aug 25, 2022

Wasu kalamai da wani babban dan siyasa yayi sun jawo magan ganu saboda tsaurin maganar kamar yadda mutane suka tabbatar

Labarin da muke samu daga jaridar Aminiya ya shaida mana cewa Ministan Cikin Gida na Uganda, Mista Kahinda Otafire ya shiga cikin tsaka-mai-wuya sakamakon wasu kalaman da ya yi da ke nuna cewa talakawa ba za su shiga Aljanna ba.

A cewar Ministan dai, talakawan ba za su Aljannar ba ne saboda sukar da suke yi wa Ubangiji wajen gabatar da korafe-korafe kowace rana.

Ministan yayin jawabi ga wani taron dalibai a Kyenjojo, ya shaida musu cewa kada su zargi Ubangiji idan sun kasa amfani da damar da Ya ba su na yakar talauci, inda ya umarce su da su
jajirce wajen samun arziki maimakon korafin da suke yi kowace rana.

Mista Otafire ya ce kuskure ne mutane su rika gabatar da korafe-korafe
da kuma zargin Ubangiji ba tare da tashi tsaye wajen yin ayyukan da za su samar musu da kudade ba.

Ministan ya ce wannan hali na sukar Ubangiji da talakawa ke yi zai hana su shiga Aljanna.

Wadannan kalamai sun haifar da ce-ce-ku-ce a kasar inda wadansu malaman addinai da kungiyoyi suke zargin gwamnati da gazawa wajen samar da yanayi mai kyau da talakawa za su samu sauki daga halin kuncin da suka samu kansu.

Kasar Uganda na daya daga cikin kasashen da ke da dimbin matasan da ba su da ayyukan yi. (Rfi)

Hukuma Tafara Bincike Akan Dan Sandan Daya Bindige Abokin Aikinsa Har Lahira

Wani jami`in ‘Dan Sanda ya rasa ran sa bayan da bindigar abokin aikin sa ta tashi inda ta harbe shi, wanda ya rasu sanadin harbin da bindigar tayi masa a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kurna a hanyar ‘Yan Sandan ta komawa jihar Katsina bayan sun kammala wani aiki da suka je yi jihar Kano.

Sifiritandan ‘Yan Sanda, Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda shine kakakin rundar a jihar Kano ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

“Akwai jami`an ‘Yan Sanda na jihar Katsina wanda suka zo aiki a nan jihar Kano, wanda kuma a unguwar Kurna suna cikin tafiya a motar su bindigar daya ta tashi inda kuma bayan ta tashi ta samu wani ‘Dan Sandan da yake cikin mota din, bayan wannan lamari an daukeshi da gaggawa an garzaya da shi asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu,” in ji Kiyawa.

Yanzu haka dai wannan ‘Dan Sanda da bindigar sa ta tashi wanda ya yi sanadiyar harbin wannan ‘dayan, wanda ya yi sanadiyar ran sa, an kama shi yana hannu, kuma an fara gudanar da bincike a kan wannan zargi na kisan kai.”

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *