Bayan bullar bidiyon dan takarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a shafukan sada zumunta lokacin da yake motsa jiki ya jawo masa abun magana. Binciken Amihad.com ya tabtar mana da cewa an saki wannan bidiyon don a tabbatarwa al’ummar Nigeria cewa Tinubu lafiyarsa kalau kamar yadda ake zarrgin bashi da lafiya.
Sai dai hakan baisa mutane sun amince da wannan lamari ba inda wasu mutane suke cewa wannan bidiyo da aka sake tsohon bidiyo ne a daukoshi ake yada karya wa mutane.
Hakan yasa wasu malamai suma sukace baza’a barsu a baya ba suma sai sunyi nasu martanin kan wannan lamarin. Kamar yadda zakuji daga bidiyon da zamu kawo muku a kasa.
Mabiyan amihad.com in baku manta ba a baya mun kawo muku labarin cewa dan takarar shugaban kasa Bola Tinubu yace Ina Da Karfin Jiki, Lafiyayye Ne Ni.
Tinubu dai ya bar Nijeriya zuwa kasar Ingila, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce a kan cewa tafiyar tasa ba za ta rasa nasaba da rashin lafiya mai tsanani ba, musamman ma a lokacin da ya fito fili a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da daukacin ‘yan takarar shugaban kasa da jam’iyyunsu suka yi.
Amma a cikin faifan bidiyon, wanda ya wallafa a shafin sa na Twitter da aka tabbatar, Tinubu ya kuma bar wani takaitaccen sako, yana mai cewa, “Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa. To… a’a.
“Wannan ita ce gaskiya: Ina da ƙarfin jiki, ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake na bauta wa ‘yan Nijeriya tun daga ranar farko da na zama shugaban kasa.”
Ga bidiyon nan sai ku kalla
Sakamakon rahotannin da ake zarginsa da rashin lafiyarsa, kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar APC ta karyata jita-jitar, tare da nuna cewa Tinubu na cikin koshin lafiya.
Da yake mayar da martani ga wani hoton bogi da ya karade kafafen sada zumunta da ke nuna cewa Tinubu ba shi da lafiya, daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa: “Ku kalli tagar gilashin sa. Bari in tabbatar wa ‘yan Nijeriya masu son sanin inda Tinubu yake. Yana Landan, a gidansa.