Anga Maisana’a yana kwaikwayon muryar Ali Nuhu a wajen daukar wani sabon shiri inda yaja kunnnen matan Kannywood kamar yadda zaku gani a bidiyon dake kasa.
Shahararren ɗan wasan barkwancin nan na masana’antar Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa mai sana’a ya bayyana dalilin da ya sa shi yawan yin nasiha ga ‘yan matan Fim.
A zantawarshi da sashin hausa na gidan biki ya bayyana cewar dukkanin kalamansa yana yin su ne bisa kishi da kuma inganta sana’ar su ta wasan kwaikwayo.
Wani faifan bidiyo da ya karade kafar sada zumunta ya nuna Musa Mai Sana’a na yi wa wasu mata ‘yan Hausa fim nasiha da gargadi akan yadda ya kamata su taka a sannu a harkar domin makomar rayuwarsu.