Wata yar karamar takaddama ta barke kan batun tambaya game da wanda ya kamata ya dinga duba wayar wani a zamantakewar aure.
Shin wa ya kamata ya dinga duba wayar abokin zama, tsakanin miji da mata? Mutane da dama suna kai ruwa rana akan wannan maganar, inda ake ta tattaunawa tsakanin maza da mata.
Inda wasu ke ganin ba laifi bane idan miji ya duba wayar matarsa, inda wasu ke ganin itama idan ta duba tashi ba laifi bane, cikin wasu daga cikin mutane kuma suna ganin kowa kawai ya rike kayansa.
Domin duba wayar na abokin zama yana iya kawo matsala ko cikali a cikin zamantakewar aure, domin aure da yawa ya mutu ne sanadiyyar dube duben wayar abokan zama.
Ga Abin Da Masana Da Malamai Ke Cewa Kan Duba Wayar Aboki Ko Abokiyar Zama Na Aure.