• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Tsawon Shekara 6 Mijina Ya Kasa Min Ciki Shiyasa Na Gwada Kwazon Direba Inji Matar Auren Da Asirinta Ya Tonu

ByLucky Murakami

Oct 29, 2022

Wata matar aure ta bayyana wa duniya yadda ta yi lalata da direbanta kasancewar ta kwashe shekaru 6 da aure ba tare da samun juna biyu ba, Legit.ng ta ruwaito.

A cewa matar, babu yadda bata yi da mijin ba akan su je asibiti don a duba lafiyarsu amma ya ki amincewa, hakan yasa ta yanke shawarar tuntubar direbanta.

Ta ce yanzu haka yaransu biyu da direban, kuma abinda yasa ta sanar da duniya gaskiya batu shi ne kada nan gaba mijinta ya gane cewa ba yaransa bane.

Matar wacce asali ‘yar kasar Ghana ce ta bayyana wannan labarin nata ga TV3 Ghana inda ta ce har sau biyu direban nata ya dirka mata cikin kuma ta haifi yaransu.

An sakaya bayanai dangane da matar inda tace ta yi shekaru 6 da aure, kuma babu kokarin da bata yi ba don ta samu ciki amma abin ya gagara.

Wannan lamarin yasa ta je har gaban likita don jin idan wata matsala ce ta same ta. Amma sai ya tabbatar mata da cewa lafiyarta kalau.

Amma a bangaren mijinta, ta ce ya ki zuwa asibitin don a duba lafiyarsa. Bayan ganin haka ne ta yanke shawarar samun mafita.

Ta bayyana direbanta a matsayin mutumin kirki wanda ta kulla kyakkyawar alaka da shi har ta kai ga sun fara kwanciya da juna.

A cewarta, garin hakan ne har ya dirka mata ciki ma daya, ta haihu, ya dawo yayi mata ciki na biyu, shi ma ta haihu.

Ta bayyana cewa direbanta ya san cewa yaran nasa ne. Amma mijinta bai farga da cewa ba nashi bane yaran.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Tsawon Shekara 6 Mijina Ya Kasa Min Ciki Shiyasa Na Gwada Kwazon Direba Inji Matar Auren Da Asirinta Ya Tonu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *