Wacece Nana Hadiza Muhammadu Buhari, Wadda Ministan Shari’a, Abubakar Malami Ya Aura ranar Juma’a?
Hajia Nana Hadiza Muhammadu Buhari Ta Halarci Makarantar First Essence International School Lokacin Tana Cobham Hall Dake Birnin Kent Na Kasar Burtaniya. Ta Kuma Halarci Jami’ar Buckingham Duk A Ƙasar Burtaniya, Ta Halarci Cibiyar Horas Da Malamai Ta Kasa Dake Kaduna Kuma Ta Yi Digirinta Na Biyu Kan Ƙasa Da Ƙasa Da Kuma Dubarun Mulki.
Majiyar amihad.com Ta Shaida Mata Cewa Hajia Nana Hadiza Muhammadu Buhari Ita Ce Ɗiyar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ta Ukku Wadda Ya Haifa Da Tsohuwar Matarsa, Marigayiya, Hajia Safinatu, Wadda Yar Asalin Karamar Hukumar Mani Ce A Jihar Katsina.
Majiyar amihad Ta Nakalto Cewa Hajia Nana Hadiza Muhammadu Buhari Tana Da Shekara 41 A Duniya Kuma Ta Taɓa Auren Alhaji Abdulrahman Mamman Kurfi Kuma Suna Da Yara Shidda Tare Kafin Rabuwar Aurensu.
Yazu Dai Ita Ce Matar Ministan Shari’a, Abubakar Malami Ta Ukku, Bayan Matansa Hajia Aisha Da Hajia Fatima.
Allah Ya Ba Da Zaman Lafiya Da Zuri’a Dayyaba!