• Sat. Jul 20th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Wadanann Dalilai Zasu Sa Ku Gane Muhimmancin Auren Mace Fiye Da Daya

ByLucky Murakami

Aug 24, 2022
Dadin auren mace fiye da daya

A yau shafin amihad.com ya kawo muku cikakakken bayani na ilimi akan hikimar auren mace fiye da daya, sai ku gyara zama domin karantawa.

Allah a Aya ta 3 cikin Suratun Nisa’i yana cewa, “Kuma idan kun ji tsoron rashin yin adalci a cikin dukiyar marayu (mata) idan kuka aure su, to ku auri abin da ya yi muku dadi daga wadansu matan, biyu ko uku, ko hudu, sannan idan kuka ji tsoron ba za ku yi adalci ba a tsakaninsu, to sai ku auri daya ko kuma abin da hannayenku suka mallaka na kuyangi. Hakan shi ya fi kusa da rashin zalunci.”

Sharhi: Masu tafsiri sun yi maganganu da yawa game da ma’anar wannan aya.

Saboda haka ne aka samu ra’ayoyi daban-daban kamar haka;

1. Ra’ayi na farko:

Cewa yake yi, da can wadanda suke kula da marayu idan mata ne sukan aure su saboda kwadayin dukiyarsu ko don kada su ba su sadakin da ya cancance su.

To shi ne Alkur’ani Mai girma ya hana su aurensu in har suna jin ba za su iya yin adalci ba wajen ba su sadakin da ya dace da su.

2. Ra’ayi na biyu:

Ya ce, bai halatta ga mutum ya auri mata fiye da hudu ba, domin kuwa da can Larabawa suna auren mata sama da hudu, suna kuma ciyar da matan nasu da dukiyar marayu idan sun matsu, ta haka ne suke cin dukiyar marayu.

To shi ne Alkur’ani Mai girma ya hana su yin wannan aure na mata fiye da hudu ya kuma gargade su da su guji cin dukiyar marayu, ya kuma umarce su da yin adalci. Wannan shi ne ra’ayin Dan Abbas da Ikramatu. Dubi Tafsirin Alfaridu, Juzu’i na Daya shafi na 502.

3. Ra’ayi na Uku:

Kuma cewa ya yi, kamar yadda aka umarce su da yin adalci da rike amana game da al’amarin marayu, to kamar haka aka umarce su da su kula da al’amarin matan aure, saboda haka ne ma aka hana su yin auren mata da yawa aka kuma kayyade musu auren mata hudu kawai.

Gaba daya dai wannan aya tana magana ce game da marayu da kuma hana auren mata sama da hudu.

Tana kuma umarni da adalci, domin kuwa shi adalci yana da matukar muhimmanci cikin dukkan al’amura.

Ya kamata a nan mu dan yi magana takaitacciya game da auren mace fiye da daya.

Addinin Musulunci dai ya halatta auren mata har hudu kuma abubuwan da za mu ambata a nan suna daga cikin hikimar auren mace fiye da daya.

• Addinin Musulunci ya kayyade auren mata hudu don ya rushe al’adar Jahiliyya ta auren mata fiye da hudu.

• Adadin mata ya fi na maza saboda su maza suna yawan mutuwa wurin yaki, to shi ne aka halatta wa namiji auren mata hudu don a kare mutuncinsu.

• Yawancin maza sukan yi sha’awar wadansu matan lokacin da matansu suke cikin lalura ta haila ko ta biki, to shi ne aka halatta musu yin auren mata fiye da daya don su samu biyan bukatarsu su kuma tsira daga afkawa cikin sabo.

• Da yawa mutum yakan yi aure sai daga baya ya gane matar ba ta da lafiya, ko kuma ba za ta iya biya masa bukatarsa ba, to ka ga ashe halatta masa auren mace sama da daya zai yi maganin wannan matsalar.

• Da yawa kuma mutum yakan yi aure sai matar ta zama juya, ba ta haihuwa, kuma a fili yake cewa kowa yana so ya bar baya.

To wannan matsalar ma ya halatta wa namiji auren sama da mace daya ne zai warware ta.

• Da yawan samari ba sa son auren zawarawa, to wa zai aure su ke nan? To ka ga a nan ma sai mu ga cewa lallai halatta wa namiji auren sama da mace daya shi ne zai ba zawarawa damar aure.

• Haka ma macen da mijinta ya mutu ya bar ta.

• Haka ma marayu mata matalauta marasa galihu, mai yiwuwa ne a rasa samari masu aurensu saboda rashin galihunsu.

Yawan mata yana kawo yawan jama’a, yawan jama’a kuma yana kawo yawan arziki.

Daga abin da ya gabata za mu fahimci cewa lallai auren mata fiye da daya shi ne kawai zai magance wadannan matsaloli, sai dai kuma wannan ya dogara ne a kan sharadi biyu kuma lallai a kiyaye su kamar yadda ya kamata.

1. Na farko dai kada a auri sama da mata hudu.

2. Na biyu lallai ne mijin ya yi adalci a tsakanin matansa cikin dukkan abubuwa, ta wajen tufatarwa da ciyarwa da rabon kwana.

A nan ya kamata mu yi wani dan bayani kuma game da matan da Annabi Muhammad (Tsira da Aminci su tabbata a gare shi), ya aura, domin mu karyata da’awar nan ta Turawa da suke cewa wai ya yi son kai da ya auri mata fiye da goma.

To idan muka dubi yawan auren da Annabi (SAW) ya yi, za mu ga cewa ba aure ne wanda yake na sha’awa ba, domin kuwa duk matan zawarawa ne, kuma wadanda suka manyanta, in ban da A’isha (RA), ita kadai ce kawai budurwa.

Kowace kuma aurenta yana da wata hikima ta musamman da maslaha wanda ta shafi addini ko shari’a ko ilimantawa ko zaman tare ko siyasa.

Za mu ga ya auri Khadija (RA) yana da shekara 25, ita kuma tana da shekara 40, haka bai auri wata mace ba sai bayan rasuwar Khadija (RA), bayan sun shekara 25 tare.

Idan muka koma ga wadancan hikimomi za mu ga cewa:

1. Matan Annabi (SAW) dukkansu malamai ne wadanda suka karantar da al’ummar Musulmi sha’anin addini da zaman duniya.

2. Dalilin da ya sa ake kiransu Iyayen Muminai ke nan.

3. Zainabu bintu Jahashi, Allah ne da kansa Ya aurar wa Annabi ita da umarninSa bayan Zaidu dan rikon Annabi (SAW) ya sake ta. Dubi Suratul Ahzabi, aya ta 37.

4. Auren A’isha ’yar Abubakar da Hafsatu ’yar Umar (RA) suna daga abubuwan da suka yi sanadin dinke dangantakar kabilun Makka da Kuraishu da kuma kafa kakkarfan tubali na ginin addinin Musulunci saboda muhimmancin Abubakar da Umar da darajarsu a idon kabilun Larabawa.

5. Auren Juwairiyya da na Safiyya da na Ramlatu duk sun zo ne sakamakon kashe mazansu a wurin yaki suka kuma musulunta, ya aure su saboda tausaya musu. A sakamakon haka kabilunsu da danginsu duka suka musulunta.

Wadannan abubuwa sun isa su tabbatar da cewa yawan auren da Annabi (SAW) ya yi, Allah ne Ya halatta masa yin haka shi kadai domin wata hikima ta musamman kamar yadda muka gani, wadda karshe za ta tabbatar da kafuwar addinin Musulunci wanda aka aiko shi domin ya tabbatar da kafuwarsa.

Haka kuma Aya ta 4 cikin Suratun Nisa’i tana cewa, “Kuma ku ba wa mata sadakinsu a kan tilas. Idan suka ba ku wani abu daga cikinsa da dadin rai, to, sai ku ci shi cikin farin ciki da murna.”

Sharhi: Alkur’ani yana umarnin a biya mata sadakinsu lokacin daurin aure. Ta yiwu a ba da kudi ko wata kadara a matsayin sadaki.

Da can maza sun kasance suna wulakanta mata suna ganin ba su da wata kima, to shi ne Musulunci ya shafe wannan mummunar akida, kuma wannan sadaki hakkin mace ce, ya zama mulkinta da zarar an daura aure ta tare.

Bai kuma halatta ga miji ya karbi wani abu daga cikinsa sai dai idan ta ba shi don ra’ayin kanta da dadin ranta.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *