• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Wadannan Sune Manyan Dalilan Dayasa Sanatoci Suke Kokarin Shige Buhari Daga Mulki

ByLucky Murakami

Aug 4, 2022

Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta arewa, Sanata Adamu Bulkachuwa na Jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana dalilansu na yunkurin tsige gwamnatin shugaba Muhammad Buhari.

Daga cikin dalilan da ya bayyana a wata hira da yayi ta musamman da kamfanin labarai na BBC Hausa, yace, “Mun bi Dokar Kasa, wacce ta bamu dama mu bawa shugaban kasa damar samun cikakken ‘yan ci na shawo kan kalubalen tsaro, kuma mun ba shi kudade isassu.

“Tsarin mulki ya bamu dama, in munyi iyaka yin mu, to mu zauna mu gaya wa shugaban kasa Gaskiya, cewa ya gaza.

“Don haka, muka zauna muka tattauna, muka yanke shawarar mu ba wa shugaban kasa makonni 6 na tafiya hutun mu, akawo sauyi ga kalubalen tsaro kafin mu dawo, wanda Mun gode Allah mun fara ganin sauye-sauye a hedikwatar tsaro ta Jami’an soji.

“Duk Sanatoci sun yarda sai ‘yan kalilan da tsige shugaba Buhari bisa dokar kasa in ba a samu sauyi ba a fannin tsaron Kasar nan har muka dawo.”

A Wani Labari Kuma Buhari Ya Ja Kunnen Hafsoshin Tsaron Nijeriya Cewa “Asarar Rayukan Ya Isa Haka”

Shugaban, a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu, ya fitar a ranar Talata, bayan rahotannin da aka samu kan asarar rayuka da dama a hare-haren, ya kuma kara ba da tabbacin goyon bayan gwamnatin tarayya ga jihohi, inda ya kara da cewa “Mun ba Shugabannin tsaro cikakken ‘yanci don kawo karshen ‘yan Ta’adda da munanan ta’asarsu.”

“Na yi Allah-wadai da wadannan munanan hare-haren a kasar nan. Ina so in tabbatar wa jihohi cewa duk wani goyon baya da ya dace, don kawo karshen Hare-haren ‘yan Ta’adda daga gwamnatin tarayya zamu tabbatar musu.

“Damuwa ta a kullum tana tare da iyalan Wadanda suka rasa ‘yan uwansu da abokansu.

“Allah ya sa wadanda suka ji rauni su warke cikin gaggawa,” in ji shugaba Buhari.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

One thought on “Wadannan Sune Manyan Dalilan Dayasa Sanatoci Suke Kokarin Shige Buhari Daga Mulki”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *