‘Yan sanda a jihar Anambra a ranar Asabar sun cafke wani mutum mai shekara 30 a duniya bisa zargin yin fyaɗe ga wata tsohuwa mai shekaru 75 a duniya.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa, kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar a birnin Awka.
Yace wanda ake zargin, wanda ɗan asalin ƙauyen Eyiba ne a jihar Ebonyi, an cafke shine da misalin ƙarfe 4 na yamma ranar Juma’a a ƙauyen Nkwelle Awkuzu.
An cafke shi lokacin da yake yiwa tsohuwar fyaɗe
Mr Ikenga, yace binciken farko ya nuna cewa an kama wanda ake zargin ne yayin da yake cikin aikata laifin a gonar matar a ƙauyen Nkwelle Awkuzu.
[ads1]
Cafke wanda ake zargin ya biyo bayan neman agaji da tsohuwar tayi ne, hakan ya janyo hankalin mutanen dake wucewa da maƙwabta inda su ka garzaya zuwa wurin sannan su ka damƙe shi.
Ya sha dukan tsiya a hannun mutanen gari
Kafin a miƙa wanda ake zargin a hannun ‘yan sanda, sai da mutane su kayi masa ɗan karen duka, a cewar ‘yan sanda.
Kakakin hukumar ta ‘yan sanda yace an kai wanda ake zargin da tsohuwar da lamarin ya ritsa da ita zuwa asibiti domin duba lafiyar su.