Labarin da muke samu shine lani matashi mai suna Kazeem Muhammad ya tsere bayan kashe mahaifinsa saboda yi wa mahaifiyarsa kishiya shekara daya da ta gabata a garin Suleja da ke jihar Neja.
Wannan abu hakika ya daurewa mutane kai ganin yadda ya nuna kishi fiye da mahaifiyarta.
Dan uwan marigayin mai suna Isah ya shaida wa yan jarida cewa bayan ya kwada wa mahifin nasa falanki a ka, take Kazeem ya cika wandonsa da iska.
Ya ce, “Matashin na shaye-shaye sosai, don haka ya saba aikata abubuwan da ba su kamata ba.
“Ranar Laraba da safe ne sa-in-sa ta shiga tsakaninsa da mahifin nasa, sai ya kwada masa wani falankin katako da ke gurin, kuma take ya fadi, shi kuma ganin haka sai ya tsere.
“Mun kai shi asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma a nan take ya ce ga garinku nan,” inji dan uwan marigayin.
Ya kuma ce tuni suka sanar da hukumomin da suka kamata domin daukar mataki, sannan suka binne gawar mamacin.
Sai dai Rundunar ’Yan Sandan yankin ta ki cewa uffan a kan lamarin. Yayinda haryanzun ana jira aji ta bakinsu akan gaskiyar lamarin.
Wadannan abubuwa ne da suka saba faruwa a kasar kasar Hausa, sai dai muna rokon Allah ya kawo mana karshen wannan masifu.