Wani rahoto da muka samu ya tabbatar mana da tserewar wani magidanci bayan matarsa ta haifa masa tagwaye wanda sune na biya kuma a jere.
Hakan ta faru ne da tunanin shi wannan magidanci bazai iya da wannan al’amarin ba inda ya gudu yabar matar da yaran.
Ayayin da wasu kan iya ba da kudi masu yawa domin ganin sun samu haihuwar koda da daya ne, wasu kuwa ba su ma son ganin matansu suna haihuwa.
A kasar Uganda, an samu wani magidanci da ya tattara kayansa ya gudu daga iyalinsa, bayan da matarsa ta haifi tagwaye sau biyar a jere.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, matar mutumin mai suna Nalongo Gloria, a kwanan nan ta haifi ’ya’yanta na tara da na 10 zuwa wannan duniyar, wanda aka ce hakan ya sa mijinta, mai suna Ssalongo ya tattara kayansa ya gudu, yana mai cewa, “haihuwar ba ta lafiya ba ce kuma ba zan iya kula da ita da ’ya’yanmu ba nan gaba.”
Matar ta ce, “lokacin da na sake samun juna biyu na tagwaye, mjina ya ce wannan ya yi masa yawa kuma ya ce in koma gidanmu, inda ya yi min kora da hali kuma ba ni da lambobin wayarsa saboda na zo Kampala yin aikatau a matsayin yarinyar gida. Ya gaya min cewa idan ba zan iya haihuwar daya ba, ba zai iya kula da ni ba.”
Ta ce wata rana ta dawo gida sai ta gane cewa mijinta ya tattara kayansa ya tafi. Tun daga lokacin ba ta ji duriyarsa ba kuma tana ta fafutukar kula da ’ya’yansu.
Duk da haka ba ta yi nadama ba ga yin haihuwar kuma ta mika bukatunta ga Allah.
“Ba na nadamar haihuwar duk wadannan yaran. Na san mahaifinsu ba ya son su amma ba zan iya watsi da su ba. Duk da kalubalen da nake fuskanta, ba zan taba barin yarana ba. Ina da yakinin Allah zai yi mana tanadi.
“Na sha wahala amma Allah ne Ya san mafita,” inji Gloria A halin yanzu Nalongo tana zaune tare da ’ya’yanta bakwai, bayan manyan tagwayen biyu sun bar gidan kuma daya daga cikin sauran ’ya’yanta ya mutu a wani hadari.
Suna fuskantar makoma mara tabbas, domin mai gidan da suke haya a kwanan nan ya bayyana wa matar cewa ba ya son ganinta a gidan ko kayanta.
Yadda Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Datse Mazakutar Mijinta Da Wuƙa A Jihar Taraba
Wata matar aure mai shekara 25 ta datse mazakutar mijin ta a garin Tella da ke ƙaramar hukumar Gassol na jihar Taraba.
Matar mai suna, Halima ta tafka wannan aika-aikan ne a ranar Talata yayin da mijin ta, Umar Aliyu ke sharar barci.
Ƙanin wanda abin ya faru da shi, Shagari Umar, ya ce ihun Aliyu ne ya jawo hankulan mutane inda suka zo suka tarar da shi kwance cikin jini.
Umar ya yi ikirarin cewa, “Mun ga matarsa Halima zaune a gefen gado riƙe da wuƙar da ta yi amfani da shi wurin datse mazakutar ɗan uwanmu.
Ya ƙara da cewa ƙiris ya rage fusattaun ƴan uwan Umar da maƙwabta suyi mata duka amma, “manya sun shiga tsakani sun ce a tausaya mata saboda tana ɗauke da juna biyu kuma suka kira ƴan sanda.
A cewarsa, an garzaya da Aliyu zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, da ke Jalingo mai nisar kilomita 150 daga garin Tella.
Ya ce, da isarsu asibitin, an bawa Aliyu kulawa cikin gaggawa aka tsayar da jinin da ke zuba daga raunin bayan an masa tiyata.
Likitan da ya kula da Aliyu, Dr Kyantiki Peter Adamu, ya shaidawa manema labarai cewa an kai shi sashin waɗanda ke buƙatar kula cikin gaggawa don wani majinyaci da aka kawo bayan datse masa mazakuta.
Abinda muka yi shine tsayar da zubar jinin cikin gaggawa da kuma yi masa tiyata a inda aka masa rauni saboda ya rasa jini sosai kafin a kawo shi,” in ji shi.
Ya ce bisa ga dukkan alamu majinyacin zai murmure amma yan uwansa sun buƙaci su tafi da shi saboda haka babu abinda asibitin zai yi a kai.
Shagari ya shaidawa manema labarai cewa cewa sun ɗauke Aliyu daga FMC Jalingo ne domin su tafi da shi wani asibiti a Gombe.
Mun ɗauke ɗan uwan mu daga FMC Jalingo mun tafi da shi FMC Gombe domin ya ƙara samun kulawar da ya ke buƙata, in ji Shagari.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP David Misal ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ƙara da cewa ƴan sanda sum kama Halima sun kuma fara binciken dalilin faruwar lamarin.