• Wed. Feb 12th, 2025

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Wani Magidanci Ya Saki Matarsa Saboda Ya Kamata Tana Chatin Da Makwabcinsa

ByLucky Murakami

Aug 27, 2022

Wani labari me cike da ban mamaki da alajabi na wani miji wanda ya kama matarsa tana chatin da wani makwabcinsa wanda hakan yayi sanadiyar kawo karshen aurensa da wannan mata.

Kamar yadda amihad.com taji labari wani magidanci ya bukaci kotu ta raba aurensa da matarsa bisa zargin ta da cin amanar aure da yin hira da makwabcinsa ta shafukan zumunta.

Da yake jawabi a gaban kotun, jaridar Aminiya ta rawaito cewa, magidancin ya zargi matarsa cewa sau uku tana tafiya ta bar gidansa, ciki har da wani lokaci da ta bar gidan nasa na tsawon wata biyu.

Ya kuma zarge ta da alaka da wani makwabcinsa wanda take daukar tsawon lokaci tana hira da shi ta intanet.

Ya ce, “Lokacin karshe da ta bar gidan sai da ta dade kafin ta dawo, da ta dawo kuma sai ta kwashe kayanta.

“Na gaji da yadda take wulakanta zaman aure, saboda haka ina bukatar kwanciyar hankali,” in ji shi.

Amma a martaninsta, matar ta bayyana wa kotun cewa mijin nata, “Ba shi da hakuri, yana zargi na da cin amanar aure ba bisa hakki ba, har ya taba sawa an tsare ni a sel din ’yan sanda.

“Na yarda a raba auren, na gaji da yadda yake duka na, zargin cin amanar auren ya ishe ni haka.”

Daga karshe kotun da ke zamanta a Ighando a Jihar Legas ta raba auren saboda abin dta kaira cin amana, sakaci da aure da kuma rashin zama tare.

Shugaban kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce raba auren shi ne zai kawo karshen takaddamar, sannan ya umarci mijin da ya biya matar Naira dubu 250.

 

Talauci ko ƙeta: Yadda aka cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan cikinta kan kuɗi N243k

A wani labarin na daban kuma an cafke wata mata na ƙoƙarin siyar da ɗan ta kan kuɗi N243k.

An cafke wata mata bisa ƙoƙarin sayar da yaron ta mai shekara bakwai a duniya ga mutanen da bata san su ba kan kuɗi £4,000, (N243k)

Matar wacce ta haifi yara uku anyi zargin ta tallata ɗan na ta a matsayin na sayarwa a ƙoƙarin ta na biyan basussukan da ta ci.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *