• Sun. Sep 8th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Wani Matashi Mai Shekara 27 Zai Kai Iyayensa Kotu Saboda Sun Haife Shi

ByLucky Murakami

Aug 17, 2022

A wani Al’amari me kama da almara wanda amihad.com taci karo dashi. Wani matashi mai shekara 27 zai kai iyayensa kotu saboda sun haife shi.

Wani mai shekaru 27 a kasar Indiya yana da shirin kai iyayensa kotu sakamakon haihuwarsa da suka yi.

Raphael Samuel dan asalin garin Mumbai ne kuma ya shaida wa shafin BBCHausa kamar yadda muka samo cewa ba daidai ba ne a ce an haifi mutum domin zai ta gwagwarmaya da wahalar duniya.

Amma Mista Samuel yana sane da cewa ba zai yiwu a nemi izinin mutum kafin a haife shi ba, amma ya dage a kan cewa “ba a nemi shawararsa ba kafin a haife shi.”

Ya bayyana cewa “Tun da ba mu ce a haife mu ba, ya kamata a biya bukatunmu har karshen rayuwarmu.”

Mista Samuel dai yana da wani irin ra’ayi wanda ke kyamatar haihuwa, masu irin wannan ra’ayi na Samuel suna kira ne da a dakatar da haihuwa saboda wahalar duniya.

Ya ce idan aka dakatar da haihuwa za a wayi gari babu dan adam ko daya a duniya kuma hakan zai kawo sauki ga wahalhalun duniya.

Ya ce “Babu wani alfanu a rayuwa irin ta dan adam. Mutane da dama suna shan wahala. Idan ba dan adam a duniya, dabobbi da ita kanta duniyar za su kasance cikin farin ciki.”

Shekara daya da ta wuce, ya hada wani shafi a Facebook mai suna “Nihilanand,” wanda ke dauke da hotunansa dauke da gemu na karya, ya rufe fuskar sa, da kuma sakwanni irin na akidarsa da ke kyamatar haihuwa.

Mista Samuel ya shaida cewa ya fara irin wannan tunanin nasa tun yana dan shekara biyar.

Ya ce “Wata rana ina yaro, abin duniya ya dame ni kuma ba na so na je makaranta amma iyaye na suka matsa sai na je.

Sai na tambaye su: Me ya sa suka haife ni?’ Maihafi na bai da amsar da zai ba ni, sai na yi tunanin da ya amsa tambaya ta da ba zan ci gaba tunani haka ba.”

A lokacin da wannan akidar ta yi kamari a zuciyar Samuel, sai ya fito fili ya bayyana wa iyayensa irin wannan tunani nasa.

Ya ce iyayensa dukkansu biyu lauyoyi ne kuma a lokacin da ya bayyana masu abin da ke cikin zuciyarsa, sun yi na’am da wannan batu.

Mahaifiyarsa ta ce dama a ce ta hadu da shi kafin ta haife shi, da ba ta haife shi ba kuwa, domin lallai akwai hanakali a cikin wannan tunanin nasa.

Mista samuel ya ce mahaifiyarsa ta ce masa tana da kananan shekaru a lokacin da ta haife shi kuma ba ta san cewa akwai yadda za ta yi ba.

Amma abin da Samuel yake cewa, kowa yana da yadda zai yi a duniya.

A cikin wata sanarwa da mahaifiyarsa ta fitar watau Kavita Karnad Samuel ta bayyana cewa “na ji dadi da yaro na ya girma kuma ya zama bai da tsoro, kuma yana tunaninsa ba tare da wani ya tursasa ma sa ba, ina fata zai samu farin ciki a wannan hanyar da ya dauka.”

Mista samuel dai ya ce wannan mataki da ya dauka na kai iyayensa kotu ya yi hakan ne a kan tuna cewa ta haka ne duniya za ta zauna lafiya ba tare da bil’adama a cikin ta ba.

Shafinsa na Facebook ya ja hankali inda ya samu tsokaci da dama. Wasu sun yaba yayin da masu adawa da shi suka ce ya je ya kashe kansa ya huta da wahalar duniya.

Wasu masu adawa da matakinsa sun ce ya yi haka ne domin neman suna a duniya.

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *