Wani labari me cike da al’ajabi da muke samu shine wata karuwa mai shekaru 22, Blessing Udoh ta gurfana gaban kotu bisa zarginta da ake yi da siyar da jaririyarta mai watanni 3 a Duniya kan naira 50,000, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Blessing Udoh ta bayyana gaban kotun majistri ne dake garin Ebute Meta jihar Legas, inda alkalin kotun ya yanke hukuncin a garkame mashi ita a ofishin Yansanda.
Ana tuhumar Blessing ne kan aikata laifin Karuwanci da kuma cinikin jarirai, amma ta kekasa kasa tace Allanbaran bata da laifi a dukkanin laifukan da ake tuhumar ta dasu.
Majiyar Amihad.com ta ruwaito Dansanda mai kara Kehinde Omisakin yana bayyana ma kotu cewa Blessing ta aikata wannan laifi ne a ranar 30 ga watan Yuni da misalin karfe 6 na yamma a unguwar Abbatoir dake Oko Oba, yankin Abule Egba, na jihar Legas.
Dansan yace matar ta siyar ta jaririyar tata ne ga wata iyalan Philips James mazauna garin Oron jihar Akwa Ibom, inda ya kara da cewa sun sha kamata tana aikin kilaki.
Daga nan sai alkalin kotun Tajudeen Elias ya dage sauraran karar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.
Wani magidanci ya maka mahaifiyar matarsa, Zainab a kotun Rigasa
Wani magidanci mai suna Isma’il Ibrahim ya maka sirikansa Zainab Muhammad a kotun shari’a dake Rigasa a jihar Kaduna saboda ta hana ta dawowa gida bayan ta shafe watanni uku a gidan iyayenta.
Ibrahim Wanda ke zama a hanyar ofishin ‘yan sanda dake Rigasa ya ce Zainab ta hana matarsa dawowa gida saboda shi ba mai arziki bane.
Ya ce yana kaunar matarsa sannan yana so ta dawo gida wurinsa.
“Ina rokon kotu ta taimaka wajen dawo mini da mata ta gida.
Zainab ta ce ta hana ‘yarta dawowa dakin mijinta ne saboda rashin kula da baya yi mata.
Zainab ta ce a tsakanin wannan lokaci ‘yarta ta yi rashin lafiya amma ibrahim bai iya biyan kudin asibiti ba.
“Bayan na biya kudin magani da asibiti Ibrahim ya bar ni da kula da ‘yata a gida.
Ta ce ta hana ta komawa gida ne saboda tana so ta zauna da ita har sai ta yi watanni 6 ta tabbatar ta warke sarai tukunna.
“Matar Ibrahim za ta dawo gida idan Ibrahim ya biya ni kudaden da na kashe na asibiti da wanda na kashe wajen ciyar da matarsa na tsawon watanni 9.
Alkalin kotun Malam Abubakar Salisu-Tureta ya daga shari’an zuwa ranar 4 ga Satumba domin Zainab ta gabatar da jimlar kudaden da ta kashe.