Labarin daya shigowa amihad.com shine An Damke Mutumin Da Ake Zargi Da Yi Wa Marainiya Mai Shekara 7 Fyade A Wani Yanki Na Jihar Nasarawa.
Ana zargin wani mutum mai shekara 50 kuma ma’aikaci a Kwalejin Ilimi da ke Akwanga, Jihar Nasarawa, da yi wa wata yarinya marainiya mai shekara bakwai fyade.
Majiyarmu ta gano cewa yarinyar da lamarin ya shafa na zaune ne tare da kakanta a Unguwar Loko da ke yankin kauyen Gwanje cikin Karamar Hukumar Akwanga a jihar.
Kakan yarinyar ya shaida wa wakilinmu cewa yarinyar ita ce jika daya tilo da yake da ita.
Don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar, da ’yan sanda da dukkan hukumomin da lamarin ya shafa da su shiga cikin batun tare da tabbatar da wanda ake zargin ya fuskanci hukunci daidai da laifin da ya aikata.
Yarinyar, wadda ta rasa iyayenta shekara hudu da suka gabata, ta sanar da wakilinmu cewa a ranar da abin ya faru, bayan da ta fahimci ita kadai ce ta rage a gida sai ta fita waje ta zauna.
Ta ce wani mai suna Kawu Dan wanda suke makwabtaka da shi ya bukaci ta je ta same shi, amma ta ki.
Ta ce, “Bayan da ya tafi, sai ya sake dawowa inda ya yi kamar ya dawo dibar ruwa a rijiya. Kafin in farga, ya ja ni zuwa dakinsa ya cire mini kaya ya kwanta da ni.”
Kakan yarinyar ya ce da yamma da ya dawo gida bai tarar da jikar tasa ba.
“Da farko na yi tunanin ko garkuwa aka yi da ita. Na shiga damuwa matuka da ban gan ta ba.
“Ko da na bincika makwabtaka, a nan na ga ta fito daga dakin Dan tana dingishi. Idanunta sun yi ja, sannan ta hada zufa.
“Da na tambaye ta abin da ya faru, sai ta bayyana mini cewa makwacina, Danladi Daniel, ya ja ta zuwa daki ya yi lalata da ita.
“Nan take na hanzarta kai ta cibiyar lafiya da ke kusa inda aka gwada aka tabbatar da lallai an yi mata fyade. Haka nan, mun ga alamar jini a kamfanta da al’aurarta,” inji kakan yarinyar.
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel, ya ce an kama wanda ake zargin.
“An kama Mista Danladi Daniel, ma’aikaci a Kwalejin Ilimi da ke Akwanga, bisa zargin yi wa marainiya mai shekara bakwai fyade,” inji jami’in.
Ya kara da cewa tuni aka mayar da wanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar da ke Lafiya don fadada bincike.
Bayanai sun ce abin damuwa ne matuka yadda ake yawan samun faruwar fyade ga kananan yara a sassan jihar.
An tabbatar cewa tsakanin watan Janairu zuwa Yulin bana, an yi wa kananan yara sama da 10 fyade a sassan jihar ta Nasarawa.