• Sun. Nov 10th, 2024

Amihad.com

Number 1 Financial Education and Tech Blog

Wata Mata Ta Kama Mijinta Yana Lalata Rayuwar ‘Yarsu Me Shekara 14

ByLucky Murakami

Aug 25, 2022

Dubun wani mutum a jihar Katsina ta cika bayan da matar sa ta damke shi dumu-dumu ya na aikata fasikanci da ‘yar su mai shekaru 14 a duniya

Wata mata, Mariya Inusa, mai shekaru 35 a duniya, wadda mazauniyar kauyen Rafin-Makadi ce, a karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina, ta shigar da karar mijin ta Inusa Aliyu wajen ‘yan sanda, da laifin aikata fasikanci da ‘yar su mai shekaru 14.

Mariya ta tabbatar da wannan ta’asa da mijin ta yake aikatawa bayan da ta kama shi dumu-dumu a cikin laifi, inda ta garzaya wajen ‘yan sanda.

Ta bayyanawa ‘yan sanda cewa, daman ta jima ta na zargin wannan abu, amma gashi yau ta gani da idonta da dubu ta cika kuma kuma daman ance gani ya kori ji domin ya tabbatar ma ta da zargin da ta jima ta na yi.

Mariya ta kara samun tabbaci daga wajen ‘yar ta su bayan da ta titsiye ta akan sai ta fada mata a gaskiyar lamarain inda ita kuma ba ta boye ma ta komai ba.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah, ya tabbatar da cewa, Inusa yana nan a hannun su domin cigaba da bincike kafin su tura shi gaban alkali.

Inusa ya amsa laifin da ake tuhumar shi da shi, kuma ya ce wani dan duba ne ya ba shi wani lakani kuma idan bai aikata fasikanci da ‘yar shi ba to kuwa lakanin zai karye.

 

Yaushe Za A Fara Hukunta Masu Aikata Fyade?

Binciken da masana suka yi, sun gano cewa babu abinda ya fi ta’azara a wannan lokacin kuma yake ci wa al’umma tuwo a kwarya kamar yi wa yara kananan fyade, sannan hukunci ba ya tasiri ga mafi yawan wadanda suke aikata wannan ta’asa.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumomi da kungiyoyin kare hakkin yara na cikin gida da kuma na kasashen waje suke fafutukar ganin an kare hakkin yara musamman ta hanyar hukunta wadanda aka kama da laifin yi wa Kananan yara fyade.

Abu kamar wasa, sai kara yaduwa yake a cikin birni da karkara ta inda da wahala rana ta fito ta fadi baka ji labarin wani ya yi wa wata karamar yarinya fyade ba, ko kuma yana da wahalar gaske ka je kotu ba ka ga jami’an ‘yan sanda sun gabatar da wani da laifin yi wa yara kananan fyade ba.

Sai dai kuma wani abu da ke daure kai shi ne, ana daukar mataki abin yana cigaba da faruwa kamar wutar da ji, wani lokaci ma, za a kama mutun da wannan zargin maimakon ka ji cewa yana yi domin biyan bukatarsa sai ka tarar cewa wani boka ko matsafi ne ya ba shi sa’a ya yi lalata da karamar yarinya domin biyan bukatar duniya.

Kazalika a wani lokaci ma, sai ka ga cewa bayan an yi lalata da karamar yarinyar da ba ta san abinda duniya take ciki ba, a karshen sai a raba ta da rayuwarta domin gudun kar asiri ya tonu, wanda yanzu haka kungiyoyi sun dukufa wajen ganin wannan masifa ta yi sauki so sai.

Hakika mutane musamman a karkara suna da karancin wayewar kai wajan kai rahotan ire-iren wadanna matsaloli zuwa ga wata kungiya ko hukuma mafi kusa domin daukar mataki musamman idan wanda ya aikata laifin wani babban mutum ne ko kuma dan wani ne.

Hakan yana taimakawa wajan cigaba da zaluntar kananan yaran da ba su ji ba su gani ba, wasu saboda rashin gata sai dai gobe kiyama wasu kuma kungiyoyin sa kai da na kare hakkin dan Adam da kuma ‘yan Jarida na taka mahimiyyar rawa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, inda a wasu lokuta ake samun nasara.

Wannan annoba dai tana neman gindin zama a jihar Katsina, inda ko a shekarar 2014 sai da aka samu rahotannin fyade guda 63 kuma kimanin 21 sun faru ne a cikin birnin Katsina kafin abin ya ta’azara daga baya.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta samu rahotan fyade har guda 112 a jihar Katsina sannan ta yi nasarar gabatar da mutane 79 a gaban kuliya manta sabo domin fuskantar tuhumar ake yi masu.

A karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina a watan Mayu na wannan shekarar ta 2017 an kama wani mutun mai suna Salisu Magaji dan shekaru 57 ya yi wa yarinya yar wata bakwai fyade wanda hakan ya yi sanadiyar rasa ranta, bayan an kwantar da ita a asibitin kula da yara da mata masu juna biyu na Turai Yar’adua da ke Katsina.

Haka kuma an kama wasu mutane biyu a garin unguwar Bawa da ke karamar hukumar Danja sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara daya fyade bayan sun fizgeta daga hannun mahaifiyarta. A yayin da aka kama wani mai suna Abdul Bashir ya yi wa ‘yar shekara shida fyade, sannan ya shaidawa manema labarai cewa wani bokansa ya ya ce yi amfani da ita akan wata biyan bukatarsa ta duniya.

Kazalika a wannan watan da muke ciki rundunar ‘yan sanda sun gabatar da wani shugaban makarantar firamari (Headmaster) mai suna Sule Yusuf dan shekaru 57 a gaban kotu bisa zargin yin lalata da yaro namiji dan shekara hudu.

Wannan al’amari na faruwa fadar mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ta fitar da wata takardar sanarwa inda ta dakatar da shi daga sarautar magatakaradar Katsina.

Sakamakon yawaitar wannan matsala ta fyade ta sa bangaran shari’a a jihar Katsina suka dukufa wajan sabunta dokar nan da ta yi tana jin hukuncin shekaru goma sha hudu a gidan wakafi idan an kama mutun da laifin yin fyade sannan wanda aka kama da laifin zai biya tarar naira dubu hamsin ga iyalan wanda aka yi wa fyadan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni bincike ya yi nisa game da wannan batu kuma da zaran sun kammala za su mikashi gaban kuliya manta sabo domin fuskantar hukunci.

Akwai bukatar hukumomi su tashi kai tsaye wajen tabbatar da ganin ana hukunta wadanda aka samu da hannu wajen aikata fyade, ta haka ne kadai masu kokarin za su tsorota, domin masu iya magana kan ce ‘Da Na Gaba Ake Ganin Zurfin Ruwa.’

By Lucky Murakami

A savant on system network security and information technology with adept leadership skills.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *