Barka da wannan rana, labarin da muke samu shine wani mutum ya cinna wa gidansa wuta da gangan a Jihar Kwara saboda matarsa ta bata masa rai, kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana.
Wanda hakan ya faru ne bisa ganganci da bacin bawai tsautsayi ba, ace mutum ya cinnawa gidansa wuta saboda hali na rayuwa.
Mista Hassan Adekunle, wanda shi ne kakakin daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:28 na safiyar Lahadi a Lekki Phase One da ke unguwar Eyenkorin a Ilorin, babban birnin jihar.
Adekunle, yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce mutumin ya yi ikirarin cewa da gangan ya cinna wa gidan mai dakuna uku wuta saboda tsananin takaicin matarsa.
A cewarsa, gobarar ta kone gidan baki daya, wanda wani mazaunin yankin ya yi gaggawar sanar da hukumar kashe gobara game da lamarin.
Adekunle ya kara da cewa, daukin gaggawar da jamiāan hukumar kashe gobara suka yi ne ya sa aka shawo kan gobarar tare da hana ta yaduwa zuwa wasu gine-ginen yankin.
Olumuyiwa, a nasa jawabin, ya yi kira ga mazauna jihar da su kara sanya ido a gidajensu, ofisoshinsu, da kuma duk inda suka samu kansu.