Close Menu
    AMIHAD.COM
    • Admission
    • Education
    • Finance
    • Scholarship
    • Tech
    • Visa
    AMIHAD.COM
    News

    Ya Shigo Daki Ya Kama Matarsa Da Abokinsa Suna Cin Amanarsa

    Lucky MurakamiBy Lucky MurakamiOctober 31, 2022No Comments2 Mins Read

    Duniya ina zaki damu, wani magidanci ya tona asirin yadda ya shigo otel bazata ya taras da matarsa tana cin amanarsa da kwarto a dakin otel inda wanda ya shaida cewa dama halinta ne.

    A wannan lokaci irin wadannan abubuwa nada hau-hawa wajen faruwa tsakanin maza da mata wanda ya akamata a nemi mafita.

    Kamar yadda amihad.com ta binciko, bugun zuciya ya kama wani mutum, Udemeh Ukarette, mai shekaru 34, a yayin da ya kama matar sa, Joy Ukarett da wani kwastoman ta wani otel.

    Shekarun Udemeh da Joy 16 da aure amma ba su samu haihuwa ba, inda ta ce tayi hakan saboda ta samu ciki tunda shi mijin na ta ya kasa.

    Jaridar PM EXPRESS ta ruwaito cewa, wannan abu ya faru ne a layin Toyin Giwa na yankin Afonka Shasha da ke jihar Legas.

    Jaridar ta ce, Joy ta sanar da mijinta kuma ya aminta kafin ta kwanta da wannan kwastoman na ta, inda abin ya juya ta fara jin dadin tarayyar su shine ta cigaba.

    Da Udeme ya ce ta yanke alakar ta da wannan mutumin shine ta bayyana mijin ba za ta daina ba kuma ta ce mutumin shine babban kwastoman ta sannan ta yi ikirarin idan ya matsa ma ta za ta raba auren su ta komawa daduron ta.

    Udemeh da Joy wanda ‘yan asalin garin Anan ne na jihar Akwa Ibom sun bayyana cewa, sun nemi magani na asibiti da na gargajiya amma har yanzu ba wani labari.

    Udemeh ya kai karar matar sa kungiyar su ta ‘yan Akwa Ibom a cibiyarsu ta jihar Legas, inda aka yi kokarin a sulhunta amma Joy ta yi mursisi akan ba za ta yanke alaka da sabon saurayinta

    Sai dai ta amince za ta cigaba da zama a matsayin matar Udemeh kuma tana tarayya da saurayin na ta.

    Related Posts

    Tofah Bayan Ganin Bidiyon Tinubu Yana Motsa Jiki, Malmai Sun Fara Zazzago Martani

    January 11, 2024

    Yadda Wata Matar Aure Ta Kama Mijinta Yana Cin Amanarta Ba Kunya Ba Tsoron Allah

    December 25, 2022

    Karshen Duniya Yazo: Yadda Dalibi Ya Dirkawa Malamarsa Ciki

    December 12, 2022

    Wani Dalibi Ya Kashe Kansa Saboda Ya Kasa Mallakar Wayar Naira Dubu Hamsin

    November 27, 2022

    An Kama Likitan Bogi Daya Dirkawa Yan Mata Hudu Ciki

    November 26, 2022

    Yadda Mahaifiyar Budurwa Tasa Saurayi Ya Dirkawa ‘Yarta Ciki

    November 25, 2022
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    • About Us
    • Contact Us
    • Disclaimer
    • Privacy Policy
    • Terms & Conditions
    Copyright © 2025 AMIHAD.COM | All Right Reserved.

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.