Wannan rubutun an yi shine domin sabbin ma’aurata ko masu niyyar yin auren nan bada dadewa tare da ma’aurat masu neman karin ilimin game da harkar aure a addinin musulunci.
Yana daga cikin hanyar samun zuriya tagari yin sallah ta nafila raka’a biyu, lokacin da ka shiga xakin amarya a daren farko.
Sannan mutun ya dora hannunsa a kan matarsa, sai ya karanta addu’ar da Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya koyar.
Addu’ar kuwa ita ce: ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻰ ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﺧَﻴْﺮَﻫَﺎ ﻭَﺧَﻴْﺮَ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺃَﻋُﻮﺫُ ﺑِﻚَ ﻣِﻦْ ﺷَﺮِّﻫَﺎ ﻭَﻣِﻦْ ﺷَﺮِّ ﻣَﺎ ﺟَﺒَﻠْﺘَﻬَﺎ ﻋَﻠَﻴْﻪ
Allahumma inni as’aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alayhi, wa a’uzu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alayhi.
[41] ADDU’AR SADUWA. Haka nan ma yin addu’a yayin saduwa domin Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa
alihi wa sallam ya ce duk wanda ya yi addu’a yayin saduwar aure, idan Allah ya qaddara samun xa a lokacin saduwar, shaidan ba zai cutar/ shafe shi ba da iznin Allah.
Ga addu’ar kamar haka: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ، ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ
BismilLahi Allahumma jannibina Shaidana wajannibi Shayxana ma razaqatana.
[42] Wannan addu’ar duk yayin da ka zo saduwa da matarka ana bukatar ka da ka karanta ta, ita ma matar tana iya karantawa babu laifi.
Haramun ne saduwa da mace ta dubura. Wani hadisin ma Manzon sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce Allah ya tsine wa wanda ya sadu da matarsa ta dubura.
Wani hadisin kuma cewa ya yi wannan mutum ya bar musulunci wanda ya sadu da matarsa ta dubura.
Ya halatta mutum ya sadu da matarsa a tsaye ko a kwance ko a rigingine ko ta yi goho.
Duk dai yadda mai gidanta ya so ta yi masa, amma kada ya sadu da ita ta dubura.
Allah yana cewa: ﴿ﻧﺴﺎﺅﻛﻢ ﺣﺮﺙ ﻟﻜﻢ ﻓﺄﺗﻮﺍ ﺣﺮﺛﻜﻢ ﺃﻧّﻰ ﺷﺌﺘﻢ﴾ “Matayenku gonakinku ne ku je wa gonakinku ta yadda kuka so.” Allah bai ce ta inda kuka so ba, sai ya ce ta yadda kuka so.
Haramun ne saduwa da mace ta dubura.
Hadisi ingantacce ya tabbata ya ke cewa, “Tsinanne ne wanda ya sadu da matarsa ta dubura.
”[43] ) ﻣﻠﻌﻮﻥ ﻣﻦ ﻳﺄﺗﻲ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻲ ﻣﺤﺎﺷّﻬﻦ . ﻳﻌﻨﻲ : ﺃﺩﺑﺎﺭﻫﻦ (( Wata ruwayar ta ce duk wanda ya sadu da mai haila ko ya sadu da mace ta dubura ko ya je wajen boka ya kuma yarda da abinda ya fada masa, ya kafirce wa abinda aka saukar wa Muhammadu.
(Wato ya bar musulunci” ) ﻣﻦ ﺃﺗﻰ ﺣﺎﺋﻀﺎً، ﺃﻭ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﻓﻲ ﺩﺑﺮﻫﺎ، ﺃﻭ ﻛﺎﻫﻨﺎً ﻓﺼﺪﻗﻪ ﺑﻤﺎ ﻳﻘﻮﻝ؛ ﻓﻘﺪ ﻛﻔﺮ ﺑﻤﺎ ﺃُﻧﺰﻝ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ
Wannan hadisin ya nuna mana wanda ya sadu da mai haila ko ya sadu da matarsa ta dubura ya bar musulunci.
[44] SANYA MASA SUNA NAQWARAI
Yana daga cikin haqqin ‘ya’ya iyayensu su sanya masu suna nakwarai kamar yadda muka gani a kissar baya. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce’ “Lallai ku za a kira ku ranar alkiyama da sunayenku da sunayen iyayen ku. Saboda haka ku kyautata sunayenku (da na ‘ya’yanku)”
[45] Mafificin sunan da Allah ya fi so, Abdullahi da Abdurrahman.
[46] ﺇِﻥَّ ﺃَﺣَﺐَّ ﺃَﺳْﻤَﺎﺋِﻜُﻢْ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻋَﺒْﺪُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻋَﺒْﺪُ ﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِ
bangaren mata kuma Amatul Lahi ko Amatur Rahaman
[47]. A guji sanya mummunan suna domin za a kira mutum da mummunan sunansa ranar Kiyama.
Kuma mai mummunan suna zai tashi da xabi’u munana da mummunan hali. Wannan ya sanya a wani hadisin manzon Allah sallal Lahu alayhi wa sallam ya ce, ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﺍﻟﺪَّﺭْﺩَﺍﺀِ، ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠﻪِ ” ﺇِﻧَّﻜُﻢْ ﺗُﺪْﻋَﻮْﻥَ ﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ ﺑِﺄَﺳْﻤَﺎﺋِﻜُﻢْ ﻭَﺃَﺳْﻤَﺎﺀِ ﺁﺑَﺎﺋِﻜُﻢْ ﻓَﺄَﺣْﺴِﻨُﻮﺍﺃَﺳْﻤَﺎﺀَﻛُﻢْ
An karbo daga Abid Darda’i ya ce “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Lallai za a kira ku ranar kiyama da sunayenku da na iyayenku. Ku kyautata sunayenku.
[48] Wannan hadisin yana umurni ne a riqa kiran mutum da sunan mahaifinsa, kamar yadda zaka ga wasu mata ana kiransu da sunayen mazajensu.
Yin haka kuskure ne sava wa Allah ne da Annabinsa. Abinda yake daidai a kira su da sunayen iyayensu ko bayan sun yi aure.
Yana daga munanan sunaye kamar: Zakkuma, Humairah, Samirah, Dudu, Hurairah, Mal’unatu, Lantana, Maraqisiyyah, Safinatu, Baxxatu, Barratu,Shadiyyah, Jatthama,Huyaam,Nuhaad,Iqilima,Nadiya,Adama,Abdul- Muxxalib,Abduln-Nabee, Diana,Zaituna,Bashariyyah,Maashixa, Qamariyyah da sauransu aje a tambayi Malamai.
Suna yana bin yaro ko yarinya. Suna kyakkyawa yana da tsananin tasiri a kan ‘ya’ya haka shima suna mummuna yana da tasiri a wajen ‘ya’ya.
[49]. Taron suna da akeyi rana ta bakwai a kofar gida na maza bidia ce haka nan ma sa suna a masallaci wanda ake yi bayan sallan subahi ana raba dabbino ko goro ko minti shima bidia ne.
Amma ya halasta a fadi haihuwa da sunan yaro a masallaci ba tare da an raba komai ba, ba tare da ance ai masa addua ba, domin ya tabbata acikin Sahihu Muslim Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya fadi haihuwan dansa mai suna Ibrahim Mu’azam a cikin masallaci kuma ya sanya ma wasu yaran suna a masallaci amma ba a samo an raba dabbino ba kogoro ba ko a ce ayi masa addua bayan sallah ba.
[50] Taron suna na mata shima bidia ne, na mata ma yafi muni ya kamata duk AhlusSunnah na gaskiya ya hana taron suna na mata kamar yadda Allah ya taimaka aka daina na maza suma mata a hana su wannan shine
gaskiyan labari, duk inda bidia ta ke sharri ke aukuwa, mafificiyar shiriya ita ce shiriyar manzon Allah.
TAHANEEK Bayan an haifi yaro ana tauna dabino a diga masa ruwan dabinon a bakinsa. Yin haka Sunnah ce. Idan babu dabino wasu malaman sun ce ana iya amfani da zuma.
An ruwaito daga Abi Musa ya ce, “An haifar mani yaro, na kai shi wajen Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya sanya masa suna Ibrahim ya tauna dabino ya xiga masa a bakinsa ya yi masa addu’a ya ce Allah ya yi mashi albarka.
[51] Yadda ake Tahaneek shine bayan an tauna dabbinon za a xiga ruwan a bakin yaron sannan a goggoga masa ruwan dabbinon saman bakinsa da kasansa da harshensa da hanqansa da dasashin sa.
KIRAN SALLAH Ya shahara wajen mutane maganan kiran sallah a kunnin jariri lokacin da aka haife shi, amma sai dai bincike ya tabbatar da cewa wannan maganan ba ta inganta ba duk hadisan da su ka zo kan kiran sallah Dha’ifai ne Sheikh Kamal Abu Malik ya ce hadisan da su ka zo kan kiran sallah dukkaninsu ba su ingata ba, ba a kafa huja da su.
[52] Cikin mazajen da suka ruwaito hadisin kiran sallah akunnin jariri akwai Asim shi kumaAsim Dhaifi ni a ruwayasa, ibn Hajar ya fadi acikin Tahazib mutum ne mai rauni kuma tataccen maqarya ci ne.
[53] Akwai ruwayar Hammad ibn Shuaib ita ma Munkara ce inji Imamul Bukhari, Maganan kiran sallah a kunnin jariri ba su inganta ba.
[54] Ita kuma ruwayar Bayhaqi shi da kansa ya ce hadisin dhaifi ne.
[55] Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albani ya ce hadisan kiran sallah dha’ifai ne duba Silsilatu Dhaifa 321-393. Hadisin iqama a kunnin jariri ba shakka wajen malaman hadisi cewa hadisi nebaragulbi danjabu bai ingantaba, abin da ya ke daidai ba a kiran sallah ko Iqama a kunnin jariri.
[56] YANKA RAGO Yana da ga cikin haqqin xa ko ‘ya bayan haihuwa ana yanka wa yaro raguna guda biyu idan kuma mace ce za a yanka mata guda xaya ne.
[57] Ana yanka rago ne rana ta bakwai. Idan hali bai samu ba an so ayanka a rana ta sha hudu ko rana ta ashirin da daya kamar yadda hadisi ya nuna kuma hadisi ne ingantacce.
[58] Hakanan kuma ya tabbata manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya yanka ma sayyina Hassan raguna biyu a rana ta bakwai shima sayyidina Hussaini raguna biyu aka yanka masa.
[59] Ita Nana Aishatu Allah ya qara mata yarda ta ce ‘’ namiji raguna biyu ake yanka masa mace rago xaya.
[60] Wanda ya yanka ma xansa rago daya ana binsa rago xaya da zai yanka masa domin yadda Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya karantar raguna biyu ne mace ce rago daya.
Ana yanka rago ne ko tunkiya ko qadduwa ko bunsuru, amma ba a yanka saniya ko raqumi, kuma ana yankawa a rana ta bakwai ba ta takwas ba
[61]. Idan aka yi maka haihuwa ranar Juma’a, za ka yanka rago ne ranar Alhamis. Domin idan ka qirga zaka ga ranar Alhamis ce bakwai. Muddum ya kai Juma’a to ya zama kwana takwas ke nan.
[62] Kuskure ne rashin qirgawa da ranar haihuwa. Tun daga ranar haihuwa zaka qirga, ba a yanka saniya ko raqumi.
Qanwar nana A’ishatu ta haihu aka ce a yanka raqumi sai Nana A’ishah ta ce Allah ya tsare ta manzon Allah bai ce
ba.
Zance mafi daxi dai ba a yanka Sa ko Saniya ko Raqumi ba. Wanda ya yanka kafin rana ta bakwai ya sava ma shara’ar musulunci, hadisi dai ya ce rana ta bakwai ibn Hazmin ya ce sam bai halasta ba yankawa kafin rana ta bakwai.
[63] matashiya/shin ya halasta karya qashin ragon suna Ba kyau karya qashin ragonsuna ana so ne a zare naman
amma kar a datsa ko karya qashin, ana dafawa ne da qashin sai a savule namanwannan ruwayar ta zo cikin Bayhaqi da Musannaf naAburRazaq, Hafiz ya tabbatarda wannan maganar a cikin Talkis.
[64] Haakim ma ya kawo wannan hadisin daga Nana Aishatu Allah ya kara mata yarda ta ce, “Yaro ana yanka masa raguna biyu yarinya rago daya ba a karya kashin ana yankawa ne rana ta bakwai ko shahuxu ko Ashirin da daya, ana cin naman ne kuma ayin sadaka da naman ragon ya kasance a rana ta bakwai.
An tambayiImam Ahmad aka ce mashi ya ya za a yi da naman ragon suna ya ce ba a qarya qashin
ragon suna ana ci ne ayi kuma sadaka da shi.
[65] Imam Malik ya ce “ ba balla kashin ragon suna ba a sayar da fatansa ko namansa sannan ya ce ba yanka gurguwa ko mai ballallan kaho.
[66] Sheikh Mustafal Adawi ya tabbatar da ingancin hadisin a cikinta’aliqin da yayi ma TuhafatulMaulud na ibn Qaym ya cehadisi ne ingantacce, ba aqarya qashin ragon suna, rashin karya qashin yanataimakawa wajen tarbiyan
yara.
[67] YADDA AKE RABA NAMAN RAGUNNAN SUNA Ana ba anguwan zoma karfata (kafan gaba) wanzami shima
ana bashi, ita kuma mai jego abata rabi idan namiji ne anyanka raguna biyu sai aba mai jego guda xaya xayan
kuma aba anguwan zoma karfata, wanzami shima a ba shi nasa rabon.
Bayan da Manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ya yanka ma sahabi Hassan raguna biyu, sai
sahabi Aliyu Allah ya kara masa yarda ya kyautar da karfata ga unguwar zoma.
[68] YI WA JARIRI ASKI Ana yi wa jinjiri ko jinjira aski a rana ta bakwai, shi ma ya tabbata a karatarwar manzon Allah sallal Lahu alayi wa alihiwa sallam.
Kin yi wa ‘ya’ya aski saba wa Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallamne. Bayan askin sai a shafawa jariri/jaririya man za’afaran akansa ko akanta, sai kuma ayi sadaka da kwatankwacinnauyin gashin ( wato za asanya gashin a sikeli, nauyin da ya nuna sai a yi sadaka dashi: Idan kilo biyu ne, sai ka yi sadaka da azurfa biyu.)
[69] KACIYA Ana yi wa jinjiri kaciya. Wajibine ga namiji, ga mace kuwa sunna ce. Kuma mutunta macene yi mata kaciya kamar yadda mai Risalah ya ce. Kuma hadisai masu yawa sun zo suna nuna mana sunna ce yi
wa mata kaciya.
[70] Ya kuma tabbata a sunna yi wa matakaciya. Ana yin kaciyar ne rana ta bakwai da haihuwar jinjirar, yin haka Sunna ce kuma shi ne mafifici ga addini da kuma yaron.
[71] Lalle wajibi ne yin kaciya, domin babu Annabin da bai da kaciya. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Kaciya tana daga cikin Fitra ta muslunci,”
[72] Wani hadisin kuma Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “Abu biyar tarbiyya ce ta
musulunci: Kaciya da aske gashin gaba da rage gashin baki da yanke kumba da tsige gashin hammata”
[73]. ،ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟْﻔِﻄْﺮَﺓُ ﺧَﻤْﺲٌ : ﺍﻟْﺨِﺘَﺎﻥُ،ﻭَﺍﻻﺳْﺘِﺤْﺪَﺍﺩُ،ﻭَﻗَﺺُّ ﺍﻟﺸَّﺎﺭِﺏِ،ﻭَﺗَﻘْﻠِﻴﻢُ ﺍﻷَﻇْﻔَﺎﺭِ،ﻭَﻧَﺘْﻒُ ﺍﻹِﺑْﻂِ Wanda ya fara yin kaciya shi ne Annabi Ibrahim yana ban shekara tamanin (80) Allah ya umurce shi da ya yi wa kansa kaciya da fatanya, kuma ya je ya yi kaciyar da fatanyar.
[74] Shi ya sa Allah a Qur’ani ya yabe shi a matsayin mai cika alkawari. Kuma Allah a suratul Nahal ya ce mu bi tafarkin sa.
Sheikh Muhammad Nasiruddeenil Albany ya ce ijima’i ne cewa kaciya ga maza wajibi ne kuma ya tabbatar da yin kaciya a rana ta bakwai dogararsa da hadisin da Babarani ya ruwaito.
[75] Imam Ahmad ibn Hambal ya ce “kar kuci yanka wanda bai da kaciya, wanda bai da kaciya ba
a karban sallarsa da aikin hajjinsa har sai ya yi kaciya.
[76] Idan akai ma yaro kaciyaarana ta bakwai ya fi saurin warkewa kuma ta kamewa gashi kuma yin haka shine daidai, yana da kyau iyaye suyi kokari suyi ma ‘ya’yansu kaciya arana ta bakwai kamar yadda shari’a ta koyar.
Kuma a likitance yin kaciya arana ta bakwai yana da nasa fa’idan. SHAYARWA Yana daga cikin haqqin ‘ya’ya a kan iyayen su mata su shayar da su nonon da ke jikinsu.
Kada a shayar da su nonon gwangwani ko nonon shanu, Allah yana cewa, “Iyaye mata suna shayar da ‘ya’yansu shekaru biyu ga wanda ya ke so ya cika shayarwar.
[77] ﻭَﺍﻟْﻮَﺍﻟِﺪَﺍﺕُ ﻳُﺮْﺿِﻌْﻦَ ﺃَﻭْﻻَﺩَﻫُﻦَّ ﺣَﻮْﻟَﻴْﻦِ ﻛَﺎﻣِﻠَﻴْﻦِ ﻟِﻤَﻦْ ﺃَﺭَﺍﺩَ ﺃَﻥ ﻳُﺘِﻢَّ ﺍﻟﺮَّﺿَﺎﻋَﺔَ Kuma ana so a yaye ‘ya’ya da wuri yana taimaka masu wajen zamantowar su masu kwakwalwa, haka ibn Qaym ya ambata. Idan da hali a yaye su kafin su kai shekara biyu.
[78] Ana so uwa ta yawaita cin banyan dabbino yana kawonono ga jariri ko jaririya kuma yana da amfani wajen zamantuwar yaro ya kasance mai hazaqa.
Malamai sun ce yana daga cikin hikimar da Allah ya ce wa Nana Maryamu mahaifiyar Annabi Isah lokacin da ta haife shi aka ce mata ta girgiza gututtiran dabbino danyan dabbion zai fado ki xauka ki ci.
[79] ﻭَﻫُﺰِّﻱ ﺇِﻟَﻴْﻚِ ﺑِﺠِﺬْﻉِ ﺍﻟﻨَّﺨْﻠَﺔِ ﺗُﺴَﺎﻗِﻂْ ﻋَﻠَﻴْﻚِ ﺭُﻃَﺒًﺎ ﺟَﻨِﻴًّﺎ BAKIN YARO YA BUXE DA KALMAR TAUHIDI Wannan zai kasance ne ta abinda mahaifiyarsa keyawaita fadi a gaban danta ko ‘yarta. Kamar su kalmar shahada, tasbihi, sai yaro ya
taso da fadar su, amma idan mahaifiya ta kasance tana yawaita zagi, ko wasu maganganu da basu dace ba
sai yaro ya taso da zage-zage.
Yana daga cikin tarbiyya ga ‘ya’ya janyo su a jikinka da sakar masu fuska. Ta haka ne mutum zai fahimci matsalolin su har ya iya yi masu gyara.
Bakin ‘ya’yanku ya bude da kalmar shahada haqqinsu ne. An ruwato daga ibn Abbas Allah ya qara masa yarda ya
ce, “Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, ‘Bakunan ‘ya’yanku su zamanto farkon abinda zai
bude da shi kalmar ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ La’ila ha ilLalLah, kuma ku umurce su da faxar ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ La’ila ha ilLalLah lokacin da su ka zo mutuwa.
[80] Haqqin ‘ya’ya a kan iyayen su ne su tabbatar kalmar farko da bakin yaro zai buxe da ita ta kasance faxar Kalmar. ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ Wasu malaman sun ce wajibi ne a tabbatar bakinsa ya bude da kalmar hahadas Ya tabbata sahabiya UmmuSulaym tana umurtan danta Anas da faxin ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ Lailaha illalLah ta na ce masa dana ka ce ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ La’ilaha illalLah ka ce ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ Ashadu anna Muhammadar RasulilLah tana koya masa faxar wannan kalmar ne kafin yaye.
[81] Ana so uwa ta riqa ta maimaita kalmar a gaban ‘ya’yanta. Yana da kyau iyaye su kiyaye jin kide-kide
[82] domin ‘ya’yansu bakunansu zai buxe da waka, uwa idan tana zage- zage yaronta bakinsa zai buxe
da zagi.
Abinda mahaifiya ta ke yawaita faxi a gaban xantako ‘yarta, kamar su kalmar shahada, tasbihi, hamdala, sai yaro ya taso da faxar su, amma idan mahaifiya ta kasance tana yawaita zage- zage, ko wasu maganganu wadanda basu dace ba sai yaro ya taso da zage-zage.
Bayan ya iya faxin Kalmar Shada da fadin As-Hadu anna Muhammadar Rasulillah daga baya sai agaya masa ma’anarsu, kuma a nuna masa Allah yana sama kamar yadda ayoyi da hadisai suka tabbatar da cewa Allah na sama da zatinsa yana ko ina da iliminsa da ganinsa wannan itace akidar Annabi sallalLahu alayhi wa alihi wasallam cewa Allah nasama kuma itace aqidar sahabbai da tabi’ai, shiya sa Sheikh Abu Zaidul al- Qiyrawani a tabbatar da cewa Allah nasama a littafinsa Risalah tun agabatarwar sa ya kawo dalilai da ke nuna Allah nasama da zatinsa yana ko ina da ilimnsa.