Kamar yadda Gborienemi ya bada labari, matarsa ce ta shawarce shi da kada ya barnata dukiyar shi a shagalin auren su, da haka gara ya narka a kasuwancin shi.
“Masoyina, ina rokon alfarma, a shagalin auren mu, ba na so ka barnata kudin ka wajen siyan rigunan amarya, abinci, abun sha, hayar wurin shagali, kwalliya da sauran abubuwan da basu taka kara sun karya ba. Da haka, gara ka kara kudin a kasuwancin ka”
“Baya ga kudin sadaki da na biya, mata ta bata gayyaci bakin da suka kai goma ba, daga dangin uwa da uba. Mun saka tsofaffin kayan da muke da su a gida.
“An daura mana aure, sannan muka sa hannu a takardar shaidar auren mu.
“Ubangiji kadai zai maka haka. Mata irin wannan suna wahalar samu wa a zamanin nan. Amma ina tunanin ni mutum ne mai sa’a.